Kungiyar likitoci MSF sun yi kira ga kungiyoyin bada tallafi da su mike tsaye wajen mara wa gwamnati baya domin dakile yaduwar cutar diphtheria.
Kungiyar ta yi wannan kira ne ganin yadda ake faɗi cewa mutum 6,707 sun kamu a jihar Kano, 110 a Borno da 21 a Bauchi.
Jami’in yada labarai na MSF Abdulkareem Yakubu ya ce a rana kungiyar kan samu rahoton akalla mutum sun kamu da cutar sannan da mutum 280 daban da suka kamu da cutar a jihar Kano.
“Cutar ya fi kama mata da yara kananan musamman ‘yan kasa da shekara biyar da basu yi ba ko kammala yin allurar rigakafi ba a jihar ba.
Yakubu ya ce ware kudade domin samar da isassun maganin cutar, yi wa mutane allurar rigakafin cutar tare da tabbatar da cewa an yi wa yara kananan allurar rigakafin na daga cikin hanyoyin dakile yaduwar cutar.
Ya ce sauran hanyoyin dakile yaduwar cutar sun hada da wayar da kan mutane game da cutar da hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.
Idan ba a manta ba ministan lafiya Muhammad Pate ya bayyana cewa cutar ta yadu zuwa jihohi 14 a Najeriya da suka hada da Legas, Osun, Nasarawa, Kaduna, Katsina, Yobe, Bauchi, Gombe, Borno, Zamfara, Jigawa, Filato, Kano da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ya ce gwamnati ta kafa kwamiti domin tsaro hanyoyin dakile yaduwar cutar.
Pate ya ce kwamitin za ta hada hannu da gwamnatocin jihohin da cutar ta bullo domin tsaro hanyoyin da suka fi dacewa wajen kawar da cutar.
Discussion about this post