Babban Lauya Mike Ozekhome ya bayyana cewa akwai matuƙar buƙatar fara yin amfani da na’urorin fasahar zamani masu ƙarfin gaske, domin dakatar da ɓarayi satar ɗanyen mai daga Najeriya, ana keta ruwa ana tserewa da shi.
Babban Lauya Ozekhome ya yi wannan kira a lokacin da ya ke bayani Taron Shekara-shekara na Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA).
An shirya taron a Babban Filin Ƙwallon Ƙafa na Ƙasa da ke Abuja.
Ozekhome ya kuma yi kira a kafa ƙaƙƙarfar doka wadda za ta tanadi tsatsauran hukunci ga ɓarayin ɗanyen mai, domin zama darasi ga wasu.
Haka nan kuma ya bada shawarar cewa gwamnatin tarayya ta halasta haramtattun ƙananan matatun ɗanyen mai da ke cikin Yankin Neja Delta.
Satar Ɗanyen Mai: Akwai Laifin EFCC, Sarakunan Gargajiya Da Sojojin Ruwa – Ozekhome:
Mike Ozekhome ya ce irin yawan satar ɗanyen mai na maƙudan kuɗaɗe da a kullum ake yi a yankin Neja Delta, akwai laifin sarakunan gargajiya na yankin, haka su ma EFCC da sauran jami’an tsaro, duk su na da laifi.
Ya ce Sojojin Ruwan Najeriya ke da haƙƙin kare dukkan ruwan Najeriya daga hare-hare kowane iri. Sannan ga su da makamai irin na zamani da jiragen ruwa na zamani da su ke sintiri a guje.
“Idan ka na da jami’an tsaro a gidan ka, sai ɓarayi su ka shiga gidan ma ka, ai za ka ga laifin mai gadin gidan na ka.
“Don haka tunda Sojojin Sama ke da alhakin kare ruwan Najeriya daga ɓarayi, to kuwa ba za ƙi zargin su da hannu a satar ɗanyen man fetur ba.
“To ta yaya ma Sojojin Ruwa za su ce ba su san yadda ake satar ɗanyen man fetur ana cika jiragen ruwa da shi ba, kuma har nausa, su ɓace a cikin ruwa. Shin aljanun ruwa ne da za a ce ba a gan su ba?
Ya kuma zargi manyan jami’an gwamnati da satar ɗanyen, ya na cewa lamarin ya zama kamar masu ɗauke da makamai sun fi ƙarfin gwamnatin kenan ita kan ta.
“Masu satar ɗanyen man nan fa jami’an gwamnati ne, tare da ɗaurin gindin Sojojin Ruwa.”
“In banda a Najeriya, ta yaya za a kama jirgin ruwa ɗauke da man biliyoyin nairori, amma a ci tarar ɓarayin ɗanyen man Naira 500,000?” Inji Ozekhome.
Discussion about this post