A yau 26 Ga Agusta ake ayyana cewa shi ne Ranar Hausa ta Duniya. A duk inda Bahaushe ya ke a duniya, ya na alfahari da wannan rana. Musamman ma masu sha’awa ko masu maida hankali ga bunƙasa harshen da kuma kishin al’adun Hausawa.
Waɗanda su ka fi yayata wannan rana dai akasari su ne gungu ko gamayyar marubuta, manazarta, masana tarihi, ‘yan jarida da sauran masu bada himma wajen yaɗa batutuwa na Hausa a soshiyal midiya
A wannan rana, ba a bar PREMIUM TIMES Hausa ba wajen taya Hausawa murnar zagayowar Ranar Hausa ta Duniya.
Banda murna, har guzirin tsaraba ta ke ɗauke da shi domin Hausawa – har ma da duk wani mai jin Hausa.
Bahaushe Mai ‘Ya’ya Da Yawa: Guda Nawa Ka Sani? Su Wa Ke Ba Ka Sani Ba?
‘Yan siyasa. ‘Yan ƙwallo. ‘Yan kasuwa. ‘Yankama. ‘Yan kokawa. ‘Yan gambara. ‘Yan caca. ‘Yan jagaliya. ‘Yandaudu. ‘Yan fashi. ‘Yan wala-wala. ‘Yan bori. ‘Yan dambe. ‘Yan takife. ‘Yan Izala. ‘Yan Ɗarika. ‘Yan Ƙadiriyya. ‘Yan Tatsine. ‘Yan Tijjaniyya. ‘Yan Shi’a. ‘Yan Ƙala-ƙato. ‘Yan sharo. ‘Yan mata. ‘Yan ƙwarto. ‘Yan bumburutu. ‘Yan cuwa-cuwa. ‘Yan ci-rani. ‘Yan gudun hijira. ‘Yan alewa. ‘Yan ƙwadago. ‘Yan barema. ‘Yan kiya-kiya. ‘Yan zamani. ‘Yan ga-ruwa. ‘Yansambo. ‘Yan kurkutu. ‘Yan amshi. ‘Yan rawa. ‘Yan fito. ‘Yanruwa. ‘Yan birni da ‘Yan ƙauye.
‘Yankoli. ‘Yan tasha. ‘Yan gambara. ‘Yan kacakaura. ‘Yan sanda. ‘Yan Ƙato-da-gora. ‘Yan ƙwaya. ‘Yan wiwi. ‘Yan giya. ‘Yan sumogal. ‘Yan sane. ‘Yan bindiga. ‘Yan samame. ‘Yan cori. ‘Yan kiri. ‘Yan kamasho. ‘Yan Boko Haram. ‘Yan Alƙa’ida. ‘Yan Taliban. ‘Yan bori. ‘Yan duba. ‘Yan farauta. ‘Yan Zariya. ‘Yan’awaki, ‘Yan fim da ‘Yan jarida.
Ga wasu ‘ya’yan…
‘Yan aljanna, ‘yan wuta. ‘Yan yaga-riga. ‘Yan su. ‘Yan ƙabalu. ‘Yan sadalu. ‘Yan sama jannati. ‘Yan santsi. ‘Yan taɓo. ‘Yan NEPU. ‘Yan ba-ruwan-mu. ‘Yandoka. ‘Yan tsurku. ‘Yan buyagi. ‘Yan iska. ‘Yan baranda. ‘Yan Kwankwasiyya. ‘Yan Buhariyya. ‘Yan maza. ‘Yan duniya. ‘Yan kwanta-kwanta. ‘Yan makaranta. ‘Yandoka. ‘Yan baka. ‘Yan babule. ‘Yan Salafiyya. ‘Yan Fityanu. ‘Yan raraka. ‘Yan Hisbah. ‘Yan KAROTA. ‘Yan Agaji. ‘Yan acaɓa. ‘Yan bursuna. ‘Yan sholisho. ‘Yan kalare. ‘Yan a-mutu. ‘Yan ƙunar-bakin-wake.
‘Yan amshin-Shata. ‘Yan maula. ‘Yan A Daidaita Sahu. ‘Yan Majalisa. ‘Yan ƙungiya. ‘Yan gudubale. ‘Yan ƙwalisa. ‘Yan burazas.
‘Yan tsugudidi. ‘Yan ragabza. ‘Yan ƙwallo. ‘Yan gulma. ‘Yan bankaura. ‘Yan ludo. ‘Yan gwangwan.
‘Yan jagaliya. ‘Yan ragabza. ‘Yan wala-wala. ‘Yan raraka. ‘Yan Najeriya. ‘Yan Nijar. ‘Yan Togo. ‘Yan Nehu. ‘Yan ƙanana. ‘Yan gurasa. ‘Yan sholisha. ‘Yan giya. ‘Yan ƙwaya. ‘Yan rakiya. ‘Yan ɗaukar amarya. ‘Yanbiyu. ‘Yan nanaye. ‘Yan ƙaƙale. ‘Yan babbaka. ‘Yandusa. ‘Yan dandatsa. ‘Yan gado.
Discussion about this post