NAIRA TA SHIGA UKU SAU UKU: Masana sun bada shawarar yadda gwamnati za ta hana darajar Naira komawa daidai ta takardar tsire ko balangu
ASHAFA MURNAI
Karin maganar da Bahaushe ke cewa, ‘idan ka ji ana sa-toka-sa-katsi, to baba ce ba ta ji a wurin rini ba’, ta yi daidai a halin da ake ciki yanzu da Naira ke ci gaba da fuskantar zubewar daraja a duk lokacin da ta yi goyayya da dala a kasuwannin canjin kuɗi.
Ganin halin da Dala ke ciki ne wasu ƙwararrun masana da ake kira ‘Agora Policy’ da ke Abuja, sun fito da rahoton shawarwarin da su ka ce idan aka yi amfani da su, to Naira za ta tsira da mutuncin ta, har darajar ta ta koma kamar da can baya.
Masanan sun ce idan CBN ya yi amfani da shawarwarin, to za a iya cimma burin da ake ƙoƙarin yi na hana Naira ci gaba da zabgewa.
A cikin wani sabon rahoton da ‘Agora Policy’ ya fitar a ranar Litinin, ya ce Najeriya na buƙatar a ƙara angizo Dala a cikin ƙasar nan, ta yadda tattalin arzikin ƙasar nan zai samu hada-hadar ruwan kuɗi masu yawan da za su sa Dala ta daina yin ƙaranci.
Dala dai ta ƙara yin daraja a Najeriya, tun bayan da ta yi tsada daga N780 a kasuwar ‘yan canji, zuwa har Naira 960 a makon jiya.
A kasuwar hada-hadar zuba jari kuwa, Dala ta tashi daga N465 a farashin gwamnati a cikin Mayu, 2023 zuwa N780, farashin da take a bankuna yanzu.
Masanan sun ce don gudun kada a kullum a riƙa tuma tsalle a wuri ɗaya, ya kamata duk wani tsare-tsarwen tattalin arziki a riƙa yin sa kafaɗa-da-kafaɗa da lamarin musayar kuɗaɗen waje da tsarin hada-hadar kuɗaɗe.
Faɗuwar Darajar Naira: Ana Kukan Targaɗe Kafa Ta Karye:
‘Agora Policy’ ya fito da waɗannan shawarwari da ma wasu masu yawa, a daidai lokacin da aka bayyana wani labari maras daɗin ji cewa ashe “Cikin 2022, CBN ya ramto maƙudan kuɗaɗe a bankuna biyu na Amurka, JP Morgan da Goldman Sachs.
A sabon rahoton baya-bayan nan da CBN ya fitar, ya bayyana cewa cikin 2022 ya ciwo bashin Dala Biliyan 7.5 daga bankunan Amurka biyu, JP Morgan da Goldman Sachs.”
Masanan sun ce wannan giriftun kinkimo ramcen Dala biliyan 7.5 daga Amirka da CBN ya yi, zai iya sa Naira kasa tsayuwa da ƙafafuwan ta a kasuwanni, a duk lokacin da ta haɗa kafaɗa da Dala.
Saboda haka sai masana su ka ce yanzu ne daidai lokacin da za a gaggauta a daki ƙarfe a lanƙwasa shi tun kafin ya yi sanyi, ya kasa lanƙwasuwa.
Sun ce akwai buƙatar samar da masu zuba jarin maƙudan kuɗaɗe daga waje, yadda Dala za ta wadata.
“Hakan zai yiwu ta hanyar samun waɗanda za a haɗin gwiwa da su, domin a samu wadatar jari sosai a cikin ƙasar nan.”
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gana da Gwamnan CBN a gaggauce, ganin yadda darajar Naira ke ci gaba da faɗuwa.
Shugaba Bola Tinubu ya fara razana ganin yadda darajar Naira ke ci gaba da zubewar da ba ta taɓa yi ba a duniya.
Wannan razanar ce ta kai shi ga yin ganawar gaggawa a Shugaban Babban Bankin Najeriya, Folashodun Sonubi a ranar Litinin.
Sun yi ganawar ce ganin yadda Naira kaɗan ta rage ta kai N1,000 ke daidai da Dala 1 a kasuwar ‘yan canji, yayin da a kasuwar hada-hadar zuba jari kuwa, ta doshi Naira 800 a dala ɗaya.
A wurin taron dai su biyun sun tattauna yadda za a farɗaɗo da Naira a kasuwa, yadda idan ta na tafiya ba sai ta riƙa dogara sanda ko ana yi mata tatata ba.
Bayan kammala taron Shonubi ya shaida wa manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa cewa, “Shugaban Ƙasa ya damu ƙwarai da halin da Naira ta tsinci kan ta.”
Sai dai shi kuma ya ce ya yi amanna faɗuwar darajar Naira ba don yawan neman ta ne da ake yi ba, sai kawai saboda ci gaba da saɓat-ta-juyat-tar da ake yi wa dala a kasuwannin ‘yan canji.
Discussion about this post