Hukumar SSS da na Gidajen Kurkuku sun kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele.
Arangamar ta faru a harabar Babbar Kotun Tarayya ta Legas, a ranar Talata, bayan bada belin Emefiele.
Ɓangarorin biyu sun so ba hammata iska, a rigmar waɗanda suka dace su tafi da Emefiele, Kafin a karbi belin sa.
SSS sun hana a tafi da Emefiele kurkuku, tare da cewa wata kotu ta ba su sammacin sake kama shi.
Kafin a nan, an bada belin Emefiele, ta ce bai aikata laifukan da za a ci gaba da tsare shi ba.
Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta bada belin tsohon Shugaban Babban Bankin Najeriya,
CBN, Godwin Emefiele.
SSS sun gurfanar da shi a ranar Talata, shi ne
lauyan sa ya ce a ba shi beli.
Mai Shari’a ya ce za a iya belin Emefiele a kuɗi ₦20,000,000.00.
SSS sun gurfanar da Emefiele kotu, a madadin Gwamnatin Tarayya, ta gurfanar da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Emefiele a kotu.
SSS sun maka shi Babbar Kotun Tarayya, inda ake zargin sa da mallakar bindiga da harsashe.
An gurfanar da shi a ranar Alhamis, amma ba a sa ranar da za a fara shari’ar ba.
Ana tsare da shi tun a ranar 10 Ga watan da ya gabata, har kotu ta yi gargadi a sallame shi Ko a gurfanar da shi.
Sai dai kuma maimakon a ga zargi da ake yi masa da ta’addanci da farko, ya ana tuhumar sa da mallakar hargitsa bindiga da harsashi.
A farkon wannan makon Babbar Kotun Tarayya ta ce wa SSS ‘Ku gurfanar da Emefiele a kotu, ko ku sake shi.’
Babbar Kotun Tarayya ta gargaɗi SSS cewa su gaggauta sallamar tsohon Gwamnan ta saɓa doka ce ƙarara.
Lauyoyin sa su ka garzaya kotu domin su yi bayani cewa SSS sun toshe hanyoyin ganawa da Emefiele ɗin.
Bayan kama shi, wasu ‘yan raji su ka ce EFCC da ICPC ke da alhakin su kama Emefiele, amma ba aikin SSS ba ne.
Discussion about this post