Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta bada belin tsohon Shugaban Babban Bankin Najeriya,
CBN, Godwin Emefiele.
SSS sun gurfanar da shi a ranar Talata, shi ne
lauyan sa ya ce a ba shi beli.
Mai Shari’a ya ce za a iya belin Emefiele a kuɗi ₦20,000,000.00.
SSS sun gurfanar da Emefiele kotu, a madadin Gwamnatin Tarayya, a kotu.
SSS sun maka shi Babbar Kotun Tarayya, inda ake zargin sa da mallakar bindiga da harsashe.
An gurfanar da shi a ranar Alhamis.
Ana tsare da shi tun a ranar 10 Ga watan da ya gabata, har kotu ta yi gargadi a sallame shi Ko a gurfanar da shi.
A farkon wannan makon Babbar Kotun Tarayya ta ce wa SSS ‘Ku gurfanar da Emefiele a kotu, ko ku sake shi.’
Babbar Kotun Tarayya ta gargaɗi SSS cewa su gaggauta sallamar tsohon Gwamnan ta saɓa doka ce ƙarara.
Lauyoyin sa su ka garzaya kotu domin su yi bayani cewa SSS sun toshe hanyoyin ganawa da Emefiele ɗin.
Bayan kama shi, wasu ‘yan raji su ka ce EFCC da ICPC ke da alhakin su kama Emefiele, amma ba aikin SSS ba ne.
Cikin su har da tsohon Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA), ya bayyana abin da ya kira “damuwar sa”, dangane da kamun da Hukumar Tsaro ta SSS ta yi wa dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Agbakoba ya ce babu wani ƙorafi don an dakatar da Emefiele, amma dai shi bai ga dalilin da zai sa SSS su kama shi ba, tunda su dai babu ruwan su da shiga lamarin laifukan da su ka shafi harkokin tattalin arziki ko kuɗaɗe.
“Aikin SSS shi ne tabbatar da tsaron cikin gida, wato cikin ƙasa. To me zai kai su ga kama Emefiele?
“Abin mamakin shi ne yadda sauran hukumomin da ke da haƙƙin binciken harkokin zambar kuɗaɗe su ka yi shiru, har yau ba su ce komai ba dangane da Emefiele, tun bayan dakatar da shi. Sai kawai ji mu ka yi SSS sun ce ya na hannun su. In dai ba zargin aikata zagon ƙasa ga gwamnati ba, me zai kai SSS su kama shi?” Inji Agbakoba.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin kama Emefiele da SSS yi, sannan aka jefa shi magarƙama bayan Tinubu ya dakatar shi.
A cikin labarin kuma an bayyana yadda SSS su ka zarge shi da laifin taimaka wa ‘yan ta’adda da kuɗaɗe, amma kotu ta hana kama shi a cikin Disamba, saboda rashin ƙwaƙƙwarar hujja.
Discussion about this post