Kungiyar IPOB da na ESC sun gamu da fushin babban hafsan dakarun Najeriya Taoreed Lagbaja, inda sojoji na karkashin 63 Birged suka bi su har moboyar su a cikin kungurmin daji suka dagargaza su.
Sannan kuma sun kama manyan bindigogi da wasu makaman ma su yawa.
Darektan yada labarai na rundunar sojin Najeriya, Brig.-Gen. Onyema Nwachukwu, ya bayyana haka a wata sanarwa da ofishin sa ta fitar ranar Asabar.
Nwachukwu ya ce sojoji da DSS sun dira wa ‘yan IPOB din ne tun da sanyin safiya, inda suka rika yi musu ruwan wuta ta ko’ina. IPOB sun yi kokarin maida musu da martani amma da yake ruwa ba tsarar kwando na ne, abin ya fi karfin su sai suka arce.
Sojojin sun kama mutum daya daga cikin IPOB din sannan sun kama bidigogi, da tuta, Adduna, da bindigogi masu dogon linzami dabamabamai.
Discussion about this post