• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    RANAR ‘YANCI: ‘Yan Najeriya mazauna Landan sun nemi a yi wa gwamnatin NNPP a Kano adalci

    JAllI-JOGAR BELIN DIEZANI A KOTUN LANDAN: Kotu ta hana Diezani fita yawon dare, da rana ma an ce ta maƙala na’urar gane duk lungun da ta shiga

    Ƴan sanda sun damke wasu abokai ƴan kungiyar matsafa dake tsafi da kawunan mutane a Ilori

    Yadda ƴan sanda suka kama Ibrahim da ya yi garkuwa da Fatima, ya ƙarɓi kuɗi kuma ya yashe ta a Zariya

    Kotu ta kori gwamna Sule na Nasarawa, ta ce PDP ce ta yi nasara a zaɓen gwamna

    Ku fito ku ceci mutanen jihar Kaduna kamar yadda kuka yi a zaben majalisun Tarayya da na sanatoci – Isah Ashiru

    An yi mana kwange a hukuncin kotu, za mu daukaka kara – Ashiru

    SSS

    TAKE HAƘƘIN ƊAN ADAM: Yadda SSS suka riƙa faffalla min mari, suka ja ni ƙasa girrrr, don kawai na ce su bi doka – Lauya Ogbankwa

    Muna ƙarancin malamai, a janye dokar hana ɗaukar sabbin malamai da gwamnatin tarayya ta ƙaƙaba – Jami’ar ABU

    TONON ASIRI: An kama wani Dagaci cikin gungun mahara a lokacin batakashi da ‘Yan sanda

    ‘Yan bindiga sun kashe mutum shida a Kaduna

    Almajirai

    UNICEF ta saka Almajirai sama da 20,000 cikin rajistar tsarin agaza wa marasa karfi a Katsina

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    Hukumar CAF za ta binciki yadda mahaifiyar ɗan wasa ta mutu cikin 1986, shi kuma ya ce atabau cikin 1990 ta haife shi

    A karo na Uku, Moroko za ta ɗauki baƙuncin gasar cin kofin kwallon ƙafa na nahiyar Afrika a Janairun 2025

    NFF ta sake nada Chris Danjuma a matsayin kocin Falconets

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    JERIN SUNAYE: Jami’o’i 51 da ba za su dauki dalibin da ya ci kasa da maki 180 a jarabawar JAMB ba

    TSARIN BAI WA ƊALIBAI RAMCE: Abubuwan da suka wajaba ɗalibai da iyaye su sani

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

No Result
View All Result

BARKEWAR CUTAR DIPHTHERIA: Kano ce ke gaba wajen yawan masu fama da cutar, yayin da mutum 836 suka kamu a Najeriya, 80 sun mutu

Mohammed LerebyMohammed Lere
July 22, 2023
in Kiwon Lafiya
0
CUTAR DIPHTHERIA: Kano ce a gaba, mutum 123 sun rasu, 38  na kwance a asibiti

Najeriya ta samu adadin mutane 836 da aka tabbatar sun kamu da cutar, yayin da 80 suka mutu daga diphtheria tsakanin Mayu da Yuni 2023.

Bisa ga rahoton cutar diphtheria da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta fitar a ranar Asabar, an tabbatar da adadin wadanda suka kamu da cutar a kananan hukumomi 33 a cikin jihohi bakwai da FCT a kasar nan.

Bisa ga sakamakon rohoton bincike da NCDC ta yi nazari a kai, an samu mutum 2,455 da ake zargin sun kamu da cutar daga jihohi 24. Sannan kashi 71.5 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar yara kanana ne masu shekaru 2 – 14.

Bisa ga rahoton, jihar Kano ce ke da adadin mutum 819 daga cikin mutum 836 da suka kamu da su.

Jihar Legas ce ta zo ta biyu a jadawalin da aka samu mutane takwas, sai Yobe da Katsina mai uku da biyu.

Jihohin FCT da Osun da Kaduna da kuma Kuros Riba sun samu mutum guda.

Jihohin Kano, Yobe, Katsina, Lagos, FCT, Sokoto, da Zamfara sune ke da kashi 98.0 na wadanda ake zargi.

Gargadin Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta yi gargadi kan cewa baba da yaro kowa ya yi ta kan sa, kada ya bari cutar Diphtheria ta kama shi.

Sashen Wayarwa da Gargadi na Ɓangaren Lafiya ya yi wannan gargaɗi a ranar Litinin, ya ce kowa ya yi nesa daga kamuwa da cutar.

Sashen ya ce cuta ce da ke kisa ba tantama, wacce ƙwayoyin halittar cuta ce ke haddasa ta.

Cutar na ɗarsashi a cikin jiki daga kwana biyu zuwa biyar, amma idan ta yi tsawo za ta yi har kwana goma.

“Ya zama wajibi musamman yara kasa da shekaru biyar da dattawa sama da shekaru 60 a kiyaye sosai.”

“Da ma yara waɗanda ba a gama yi masu allurar rigakafi ba, har jama’a su guji cinkoso da ma’amala da ƙazanta.

“Masu yawan fama da rashin lafiya su yi hattara. Masu tafiya a inda cutar ta shiga, a yi hattara. Haka a wurare da ba masu lura da harkokin lafiya.”

Cutar Diphtheria:

Cutar Diphtheria cuta ce da ƙwayoyin cutar bacteria mai suna ‘Corynebacterium’ke haddasa ta.

Cutar ta fi saurin kama yara da manya, musamman waɗanda ba su yi allurar rigakafin cututtuka da ake yi wa yara ba.

Cutar kan kama maƙogaro, hanci sannan wasu lokuta har za a farga mutum na yakunewa.

Cutar ya fi yaɗuwa idan ana yawan zama kusa da waɗanda suke ɗauke da ita, idan mai ɗauke da cutar ya riƙa yin tari ko atishawa a tsakanin mutane.

Alamun cutar sun haɗa da zazzabi, majina, ciwon makogoro, idanu su yi jajawur, tari da kumburin wuya.

Wasu lokuta mai fama da cutar zai riƙa ganin wasu farin abubuwa na fitowa a kusa da maƙogaron sa wanda ke hana mutum iya yin numfashi.

Hanyoyin Samun Kariya Daga Cutar:

1. Yin allurar rigakafi.

2. Saka takunkumin fuska, musamman idan za a shiga cikin mutane.

3. Toshe baki da hanci idan za a yi tari ko atishawa.

4. Tsaftace muhalli, wanke hannu da ruwa da sabulu a kowani lokaci.

5. Zuwa asibiti idan aka kamu da zazzaɓi, ko idan ba a gane lafiyar jiki ba.

Tags: AbujaDiphtheriaKananaKanoLabaraiNCDCNewsPREMIUM TIMESYara
Previous Post

Rajistar sunayen masu karɓar tallafi ta ƙasa ba sahihiya ba ce – Gwamnoni

Next Post

IPOB sun gamu da fushi Lagbaja, sojojin sun dagargaza maboyar su a Delta, sun kama manyan bindigogi

Mohammed Lere

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • RANAR ‘YANCI: ‘Yan Najeriya mazauna Landan sun nemi a yi wa gwamnatin NNPP a Kano adalci
  • Fasinjoji 40 sun nitse cikin ruwa, bayan kifewar jirgin su a Kogin Yauri
  • DALLA-DALLA: Yadda aka cimma yarjejeniya tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago
  • JAllI-JOGAR BELIN DIEZANI A KOTUN LANDAN: Kotu ta hana Diezani fita yawon dare, da rana ma an ce ta maƙala na’urar gane duk lungun da ta shiga
  • RA’AYIN PREMIUM TIMES: NAJERIYA@63: Lokacin Tashin Babban Yaya Tsaye Ya Yi, Ko Kuma Ya Dawwama A Girman Kwabo

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.