Kotun sauraren kararrakin cin zarafin mata da yara kanana dake Ikeja jihar Legas a ranar Laraba ta fara shari’ar dan shekara 17 da ya yi garkuwa tare da yi wa ‘yar shekara 15 fyade.
An grufanar da matashin a gaban kotun bisa laifuffukan da suka hada da yin garkuwa da fyade.
Lauyan da ta shigar da karan Abimbola Abolade ta bayyana cewa matashin ya aikata wannan ta’asa ne tsakanin ranar 11 zuwa 15 ga Yuni a layi 41 hanyar Olajumoke, Ikotun.
Abolade ta ce a tsakanin wadannan ranaku matashin ya kulle yarinyar a cikin dakinsa ya ba ta lemu ta sha wanda ya gauraya da maganin barci domin ya samu daman yin lalata da ita.
Bayan kotun ta tabbatar matashin dan shekara 17 ne alkalin kotun Abiola Soladoye ta bada umarnin tura shari’ar zuwa kotun dake sauraren kararrakin da suka shafi iyali domin yanke masa hukunci.
Soladoye ta kuma yanke hukuncin cewa matashin zai yi zama a gidan marayu dake Adigbe jihar Ogun.
Ta ce za a ci gaba da shari’a ranar 18 ga Oktoba 2023.
Discussion about this post