Kungiyar likitocin MSF sun kula da yara 10,200 dake fama da yunwa a yankin Arewa maso Yammacin kasar nan a cikin watanni hudu da suka gabata.
MSF ta kuma ce a tsakanin wannan lokacin ta bai wa yara 51,000 maganin inganta garkuwar jiki a yankin.
Kungiyar ta koka da rashin isassun ma’aikata da kayan aiki a yankin sannan tana fargaban cewa rashin daukan mataki na iya kawo koma baya a ci gaban da aka samu na inganta lafiyar yara kanana a yankin.
Jami’in yada labarai na MSF Abdulkareem Yakubu ya ce an samu yara kashi 26% dake fama da yunwa a shekarar 2023 wanda haka ya Dara yawan da aka samu a shekarar 2022.
Yakubu ya ce MSF ta bude asibitin kula da yaran dake fama da yunwa 13 baya ga 32 din da take da su a jihohin Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara.
Ya ce za a samu karin yaran da za su kamu da yunwa a daminan bana musamman daga Mayu zuwa Agusta a Najeriya.
Rikicin da ake yawan fama da su a yankin Arewa maso Yamma musamman a jihohin Katsina, Sokoto, Kebbi da Zamfara ya sa mutane da dama sun zama ‘yan gudun hijira.
Rashin zaman lafiyan da ake fama da shi a Arewa maso Yamma na daga cikin matsalolin dake cutar da lafiyar mutanen yankin.
MSF ta yi kira ga gwamnati da ta kawo karshen rashin tsaro a Arewa maso Yamma tare da tsara hanyoyin kare yara daga kamuwa da yunwa.
Discussion about this post