Tsohon Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Festus Keyamo, ya ɗaukaka ƙarar hukuncin tarar Naira miliyan 10 da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta danƙara masa, bisa ƙara maras dalili da ya kai tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar.
Kafin zaɓe ne dai Keyamo ya kai ƙara kotu cewa kotu ta bayar da umarni da EFCC da ICPC su kama Atiku bisa zargin cin hanci da rashawa.
Sai dai kuma a farkon wannan makon kotu ta kori ƙarar saboda rashin hujjoji.
Keyamo ya shigar da ɗauka ƙara a ranar Talata, a Kotun Ɗaukaka Ƙara, ya nemi a sake maida ƙarar da ya shigar ɗin a sake shari’a a hannun wani alƙalin a wata kotun.
Keyamo ya maka Atiku da EFCC, ICPC da CCB, saboda ya nemi su binciki Atiku cikin awoyi 72 amma sun yi biris da shi.
Mai Shari’a James Omotosho ne ya kori ƙarar saboda a cewar sa, Keyamo ba shi da wani haƙƙin sa a binciki Atiku.
Daga nan ne aka maka masa tara ta Naira miliyan 10.
A farkon wannan makon ne dai Babbar Kotun Tarayya ta ci tarar tsohon Ministan Buhari, saboda ya yi wa Atiku sharri, ƙage da yarfe.
Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta kori ƙarar da tsohon Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Festus Keyamo ya kai ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar.
Keyamo ya maka Atiku a kotu inda ya nemi kotu ta umarci EFCC da sauran hukumomin yaƙi da cin hanci su kama Atiku kan zargin rashawar da ake yi masa.
Keyamo, wanda ya zama Kakakin Yaɗa Labaran Rundunar Kamfen ɗin Bola Tinubu a APC, ya shigar da ƙarar ce kafin zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga Fabrairu.
Amma da ya ke yanke hukunci, Mai Shari’a James Omotosho ya kori ƙarar tare da kiran ta shirme da shiriritar sharri.
A kan haka ne kotun ta ci Keyamo tarar naira miliyan 10 a ranar Litinin.
Kotu ta umarci Keyamo ya biya Atiku diyyar ɓata masa lokaci har Naira miliyan 5. Sannan kuma ya bai ICPC diyyar ɓata masu lokaci da shi Keyamo ɗin ya yi.
Haka nan kotun ta umarci Keyamo zai riƙa ɗora masu ƙarin kashi 10 duk shekara idan ya ƙi biyan diyyar cikin shekara ɗaya.
Lauyan Atiku Mike Ozekhome da lauyan ICPC, Oluwakemi Osugun ne su ka yi jayayya da ƙarar da Keyamo ya shigar.
Keyamo, Ozekhome da Odogun dai duk manyan lauyoyi ne (SAN).
Mai Shari’a ya ce ƙarar da Keyamo ya shigar ba tada wani hurumi, kawai ya ɓata wa kotu lokaci, kuma ta kauce wa bin ƙa’idar shigar da ƙararraki a kotu.
Kafin kotu ta kori ƙarar, lauyan Atiku Abubakar ya bayyana wa kotun cewa Festus Keyamo ba shi da iznin kai ƙara, domin ya kasa kawo yadda zargin da yake wa Atiku ya shafe shi.
Discussion about this post