Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf ya maida Shugaban Hukumar Sauraren Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da Hana Rashawa, Muhyi Magaji, wanda tsohon Gwamna Umar Ganduje ya kora.
Cikin wata sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Kano, Sanusi Bature ya sa wa hannu a ranar Asabar, ya shaida wa manema labarai cewa an maida Magaji kan aikin sa nan take, kamar yadda kotu ta yi umarni.
Cikin Yuli 2021 ne Majalisar Dokokin Kano ta dakatar da shi bayan ya nuna rashin amincewa a kai akanta hukumar sa daga Ofishin Akanta Janar na jiha.
Daga nan shi kuma ya kai ƙara, kotu ta ce a maida shi, amma Gwamnatin Ganduje ta ƙi bin Umarnin kotu.
Magaji ya koma ɗan Kwankwasiyya kafin zaɓen 2023.
Discussion about this post