A Wani bidiyo da ya kareda kafafen sada zumunta a yanar gizo ne aka ga wasu mutane sun yi taron dangi suka lakadawa wata budurwa da bata wuci shekaru 25 dukan tsiya saboda ta kashe ‘yar shekara biyar da wuka.
Bidiyon ya nuna yadda wata mata ta sha damara tana dukan budurwar sannan ita budurwar na roko da a kai ta ofishin ‘yan sanda.
Wannan abu ya faru ne a unguwar Works Layout dake Owerri jihar Imo ranar 28 ga Mayu.
PREMIUM TIMES ta gano cewa haka kawai wannan mata ta dauki sharbebiyar wuka ta shiga gidan da wannan yarinya ke zama tare da iyayenta ta caka mata wukan a cikinta.
Bayan luguden dukan da mutane suka yi wa wannan mata sai ta ce “Allah ne cikin Ruhu mai Tsarki ya umarce ni in bita hargida in caka mata wuka a ciki.”
“Allah dake sama ya umarce ni in kashe ta. Ruhu Mai Tsarki ya umarce ni na kashe ta.
Cikin gaggawa wata mata da ake zaton mahaifiyar yarinyar ce ta kai ‘yar asibiti sai dai likita ya tabbatar cewa ta riga mu gidan gaskiya.
Zuwa yanzu matar na tsare a ofishin ‘yan sandan jihar.
Kakakin rundunar Henry Okoye ya tabbatar cewa matan na tsare a ofishin su yana mai cewa idan aka kammala bincike za su Kai matan kotu domin yanke mata hukunci.
Discussion about this post