Hamshaƙin attajirin nan ɗan Najeriya, kuma tsohon Sanata, Ned Nwodo, ya bayyana cewa Allah ya sa ya na da sauran kwana a gaba, ƙaddarar mutuwa a ƙarƙashin teku ba ta same shi ba.
Nwodo ya ce a cikin mutane biyar da suka mutu bayan jirgin ƙarƙashin ruwa ya tarwatse da su a ranar Juma’a, har da abokin sau Hanish Harding.
Nwodo ya ce Harding ya gayyace zuwa ƙarƙashin teku, domin su gano jirgin ruwan Titanic, wanda ya nutse cikin 1912 ɗauke da mutane 1,500 masu yawon buɗe ido.
Nwodo ya ce bai samu sukunin tafiya tare da su ba, saboda wasu lamurran da suka sha kan sa.
Ya bayyana haka ne a shafin sa na Instagram, tare da yi masu ta’aziyya.
Harding ya mutu tare da attajirin Pakistan Shahzada Dawood da ɗan sa, Suleman.
Nwodo ya tuna da wani yawon bataguro da ya ce ya yi tare da Harding da ɗan sa Giles, a Tsibirin Antarctica, kudancin ƙarshen duniya, a 2020.
Discussion about this post