Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya Yi alƙawarin cewa zai yi ƙarin albashi mai kauri, domin Naira 30,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi ta yi kaɗan matuƙa.
Tinubu wanda za a rantsar a ranar 29 Ga Mayu, ya yi wannan albishir ne a cikin saƙon da ya aika wa ma’aikatan Najeriya, a ranar 1 Ga Mayu.
“Na samu alfarmar fara shugabanci a ranar 29 Ga Mayu. Ma’aikata za su samu damar a yi masu ƙarin albashi mai kauri wanda zai sa ku riƙa ɗaukar nauyin hidimomin iyalan mu, kuma ku riƙa rayuwa cikin mutunci.
A Najeriya dai yanzu naira 30,000 ce mafi ƙarancin albashi a matakin gwamnatin tarayya da jihohi, kamar yadda gwamnati ta amince tun cikin 2019.
Tinubu ya gode wa ma’aikatan Najeriya tare da jinjina masu.
Ya kuma tunatar da su ranar da ma’aikata su ka fara yin yajin aiki na farko a ƙasar nan, wato cikin 1945.
Ya ce sun yi yajin aikin ne saboda su na so a yi masu ƙarin albashi, saboda farashin kayan masarufi ya tashi, ta yadda rayuwa ta yi tsada a lokacin.
Ya kuma jinjina wa Kungiyar Kwadago ta Kasa dangane da gudummawar da ta bayar wajen dawo da dimokraɗiyya.
“Duk abin da ku ke fafutikar neman a biya maku buƙata, zai kasance ina bayan ku. Saboda a cikin daftarin manufofin gwamnati na, na bayyana yadda zan inganta rayuwar ma’aikatan ƙasar nan.
Can a Jihar Zamfara kuwa, Gwamna Matawalle zai sauka ya bar Zamfarawa a hannun ‘yan bindiga, ma’aikatan jihar na bin sa albashin wata uku.
Yayin da ma’aikatan jiha da na ƙananan hukumomin Zamfara ke bikin tunawa da zagayowar Ranar Ma’aikata a 1 Ga Mayu, har yau ba a biya su albashin watanni uku ba, yayin da ‘yan bindiga ke ci gaba da fatattakar mazauna karkakar yankunan faɗin jihar.
PREMIUM TIMES ta zanta da ma’aikata 15 na Jihar Zamfara, waɗanda su ka shaida wa wakilin mu cewa watanni uku kenan ba a biya su albashi ba.
Ma’aikatan dai sun nemi a sakaya sunayen su, saboda tsoron kada gwamnati ta bi su da bi-ta-ƙulli, sun ce wannan ne karon farko da su ka yi azumi da Ƙaramar Sallah babu albashi.
Yayin da mafi yawan ma’aikata ba a biya su albashi tun watan Fabrairu ba, kaɗan daga cikin ma cewa su ka yi su ko na watan Disamba ma ba a biya su ba.
Ƙungiyar Ƙwadago ta Jihar Zamfara ta ce ta na faɗi-tashi ba dare ba rana, domin ganin an biya dukkan ma’aikatan haƙƙoƙin su.
Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago na Jihar Zamfara, Sani Halliru, ya shaida wa wakilin mu ta wayar tarho a ranar Lahadi cewa, “idan aka haɗa da albashin watan Afrilu da ba a biya ba, to ma’aikatan Zamfara na bin albashin watanni uku kenan ba a biya su ba.”
“Abin da yanzu ake ciki a Zamfara shi ne, mu na da ma’aikatan da ba a biya su albashin wata biyu ba. Waɗannan sun fi yawa, kuma akwai ma’aikatan jiha da na ƙananan hukumomi a cikin su. Waɗanda aka biya cikin Fabrairu ba su taka kara sun karya ba.” Inji Shugaban NLC na Zamfara.
Discussion about this post