Ƙungiyar kare muradu da manufofin ƙabilar Igbo zalla, wato Ohanaeze Ndigbo, ta ƙaryata masu yaɗa ji-ta-ji-tar cewa za ta halarci bukin rantsar da Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu.
Ndigbo ta ce masu yaɗa ji-ta-ji-tar maƙaryata ne, kuma zubar wa kan su da ƙabilar Igbo ƙima da mutunci.
Cikin makon jiya ne dai Sakataren ɗaya ɓangaren ƙungiyar wadda ta rabu gida biyu, Okechukwu Isiguzoro, ya bayyana cewa “Ohanaeze za su shiga dubu-dumu bukin rantsar da Tinubu.”
‘Ba za mu halarci bukin rantsar da Bola Tinubu ba’.
Ƙungiyar kare muradu da manufofin ƙabilar Igbo zalla, wato Ohanaeze Ndigbo, ta ƙaryata masu yaɗa ji-ta-ji-tar cewa za ta halarci bukin rantsar da Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu.
Ndigbo ta ce masu yaɗa ji-ta-ji-tar maƙaryata ne, kuma zubar wa kan su da ƙabilar Igbo ƙima da mutunci.
Cikin makon jiya ne dai Sakataren ɗaya ɓangaren ƙungiyar wadda ta rabu gida biyu, Okechukwu Isiguzoro, ya bayyana cewa “Ohanaeze za su shiga dubu-dumu bukin rantsar da Tinubu.”
Isiguzoro ya ƙara da cewa “ƙungiyar Ndigbo ta na sanar da cewa duk wani tayar da jijiyar wuya da tirjiya kan zaɓen 2023 ta zo ƙarshe, a rufe banin. Kawai a tsaya kan cewa Peter Obi ne ɗan takarar mu na zaɓe na gaba. Don haka kada wanda ya ƙara jayayya da Tinubu, domin ko ya ja ba dai nasara zai iya yi ba.”
Wannan magana ta fusata Ohanaeze, inda har Kakakin Yaɗa Labarai na ƙungiyar, Alex Ogbonnia ya fito ya ce maganganun da aka ce wai Ndigbo za ta halarci taron bukin rantsar da Bola Tinubu a ranar 29 Ga Mayu, ba daga ƙungiyar ya fito ba, ƙarya ce kawai.

Discussion about this post