Gwamna mai barin gado na Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi kira ga Shugaban EFCC AbdulRashid Bawa cewa ya sauka daga muƙamin sa, domin ya bada wuri a binciki ayyukan da aika-aikar da ya zarge shi ya aikata.
Matawalle ya ce shi da wasu fitattun ‘yan Najeriya su na da shaida da hujjojin harƙallar rashawar da Bawa ya gantsara.
Sai dai Gwamna Matawalle wanda zai sauka nan da makonni biyu, bai bayyana sunayen sauran fitattun da ya ce ɗin ba.
“Akwai buƙatar Bawa ya yi bayanin wasu batutuwa, ciki kuwa har da yadda Bawa ya riƙa sayar da wasu kadarorin da EFCC ta ƙwace, ba tare da ya bi ƙa’idar da doka ta shimfiɗa idan za a sayar da kadarorin ba.” Cewar Matawalle.
Gwamnan wanda ya faɗi zaɓen karo na biyu a Zamfara, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Laraba.
Haka kuma ya yi kira ga EFCC su faɗaɗa bincike har kan manyan jami’an Fadar Shugaban Ƙasa da Ministoci, ba wai su tsaya kan gwamnoni masu harin mulki kwanan kaɗai ba.
Ya ce kamata ya yi EFCC ta riƙa faɗaɗa binciken zambar kuɗaɗe da rashawa a kowane ɓangaren gwamnati, ba wai ta riƙa tsince-tsincen wasu ɗaiɗaikun da ta ke ɗauka ta ƙyale wasu ba.
Matawalle ya ce ya na magana ne bayan an ja hankalin sa kan wata sanarwar da Bawa ya yi, wadda ya aika wa dukkan gwamnoni masu barin gado da kuma Kwamishinoni na kowace jiha masu barin gado, wadda ya sanar da su cewa EFCC za ta fara binciken su.
A kan haka ne ya ce wannan daidai ne, amma ya kamata a haɗa da manyan jami’an Fadar Shugaban Ƙasa, Ministoci da sauran manyan shugabannin hukumomi.
Matawalle ya ce akwai buƙatar a binciki yadda Bawa ya riƙa tsara yarjejeniyar maido wa gwamnati wani kaso na kuɗaɗe tsakanin sa da wasu da ake zargi, maimakon ya gurfanar da su kotu.
A farkon makon nan Matawalle ya roƙi Shugaba Muhammadu Buhari cewa kada ya bar Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya fice waje da sunan tafiya ƙarin karatu.
Ya ce idan ya tafi, guduwa zai yi, tunda akwai sauran watanni goma na wa’adin sa da bai kammala ba.
Discussion about this post