Babban Editan PREMIUM TIMES, Musikilu , ya bayyana abubuwan da su ka ja hankalin sa, har ya wallafa littafin nan ‘The Letterman’, wato Kundin Wasiƙun Sirri Na Obasanjo.
An dai ƙaddamar da littafin mai ɗauke da shafuka 492 a cikin Disamba, 2022 a Abuja.
Mojeed ya ce irin yadda aka tsara wasiƙun da yadda aka killace su da kuma abubuwan da wasiƙun su ka ƙunsa, sun ja hankalin sa zuwa ga taskace su wuri ɗaya ya wallafa su.
Ya bayyana haka ne a wani taron da ya shafi littattafai da ƙirƙirar fasaha na CORA, wanda aka yi a kantin sayar da littattafai na RovingHights, a Tsibirin Victoria.
CIkin waɗanda su ka halarta, har da jami’an CORA da su ka haɗa da Jahman Anikulapo da Toyin Akinosho, masu sha’awar karance-karancen littafai da dama, ‘yan jarida da sauran manyan baƙi.
Mojeed ya ce wata rana ce dai ya ce wurin Obasanjo dangane da wani rahoto kan ɗan siyasar nan Buriji marigayi Buruji Kashamu, makusancin Obasanjo da ya koma maƙiyin sa.
Ya ce a ranar ce ya na cikin zagayen gani-da-ido cikin ɗakin karatun Obasanjo, sai ya ci karo da inda aka killace tulin wasiƙun sirrin da Obasanjo ya rubuta a rayuwar sa ta aikin soja, har zuwa hawan sa shugabancin Najeriya.
Ya ce daga nan bayan ya fita, bayan tsawon lokaci ya koma domin ya samu amincewar Obasanjo ya wallafa wasiƙun zuwa kundin littafi.
Idan ba a manta ba, cikin Disamba PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda aka ƙaddamar da littafin, da kuma irin yabo da jinjinar da aka riƙa yi wa mawallafin da kuma kundin littafin.
‘The Letterman’: Yadda Mashahurai Suka Riƙa Jinjina Wa Kundin Wasiƙun Sirrikan Obasanjo:
Anyaoku, Kukah, Omogui, Okauru da Falola sun ce ‘Letterman’, littafin da Mojeed Babban Editan PREMIUM TIMES ya wallafa, kundin sirrika ne na musamman:
Tsohon Sakataren Ƙungiyar Ƙasashe Rainon Ingila (Commonwealth), Emeka Anyaoku; Babban Bishop na Ɗariƙar Katoliƙa da ke Sokoto, Mathew Hassan Kukah da tsohon Shugaban Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa, Ifueko Omogui Okauru sun jinjina wa ‘The Letterman: Inside the ‘Secret’ Letters of former Nigerian President, Olusegun Obasanjo.
The Letterman dai littafi ne da Babban Editan PREMIUM TIMES arankatakaf, Musikilu Mojeed ya wallafa.
Littafin ya na ɗauke da tulin wasiƙun sirri waɗanda aka rubuto wa Obasanjo ko kuma waɗanda ya rubuta.
Haka kuma ciki waɗanda su ka jinjina wa Mojeed, akwai mashahurin Farfesa Toyin Falola da kuma Dan Agbese fitaccen tsohon ɗan jaridar nan, kuma tsohon Babban Editan Newswatach.
‘The Letterman’, Littafin Kundin Wasiƙun Sirrin Obasanjo, ya na ɗauke da shafuka 492, babi 25 na wasu wasiƙun arohi da tsohon Shugaban Ƙasa Obasanjo ya rubuta da waɗanda aka rubuto masa.
Wasiƙun na bayyana irin yadda rayuwar toshon shugaban ƙasar ta ke a mizanin Najeriya, ƙasar da ya mulka ya na soja da kuma farar hula bayan ya yi ritaya.
Daga cikin wasiƙun akwai waɗanda ya rubuta manyan mutane a Najeriya da kuma cikin faɗin duniya a ƙasashe daban-daban. Da yawan su ba a taɓa ganin su ba ko kuma jin labarin abin da wasiƙun su ka ƙunsa.
Za a ƙaddamar da littafin a ranar Alhamis, 1 Ga Disamba, a Abuja. Amma waɗanda su ka rigaya su ka ga littafin har su ka yi sharhin sa tun kafin a gabatar da shi, sun jinjina masa sosai, musamman dangane da yadda aka riƙa bi tiryan-tiryan ana warware Obasanjo a wasiƙance, tun daga lokacin da ya ke Babban Dakaren Soja (GOC), Kwamandan Zaratan ‘Third Marine Commando’ da lokacin da ya shiga yaƙi, har zuwa lokacin da ya zama Shugaban Ƙasa na Mulkin Soja daga 1976 zuwa 1979.
Wasiƙun cikin Kundin Wasiƙun Sirrin Obasanjo na ɗauke da rayuwar sa lokacin da ya riƙa fafutikar rajin siyasa daga shekarun gomiyar 1970 zuwa 1999, har aka gangaro lokacin da ya yi mulkin dimokraɗiyya, daga 1999 zuwa 2007. Kai har ma bayan saukar sa daga mulki.
Yabon Gwani Ya Zama Dole:
“Musikilu Mojeed Ya Kawo Sabon Salon Taskace Tarihin Shugabannin Da Su Ka Gabata.
“Babu wani ɗan Najeriya da ya taɓa taskace bayanan tarihin rayuwar wani shugaba kamar yadda Mojeed ya taskace ta Obasanjo”
– Bishof Mathew Hassan-Kukah.
“Wannan kundin wasiƙun sirri ya burge ni matuƙa. An ɗauki hankali na sosai ta wajen yadda aka zurfafa samun damar mallaka da zaƙulo sirrikan da aka wallafa a cikin littafin. Shi ma marubucin wasiƙun ya yi ƙoƙarin taskace wasiƙun. Littafin wata kadara ce mai tsadar gaske, sannan shi kuma Mojeed ya yi ƙoƙarin yin nitso har ƙarƙashin tekun sirrikan Obasanjo, ya kwaso su ya ba mu su za mu ci gaba da kwankwaɗa.”
-Ifueko Omoigui Okauru, tsohon Shugaban Hukumar Tara Harajin Cikin Gida (FIRS).
“Musikilu Mojeed wani ɗan baiwa ne da ya yi hazaƙar fito mana da tulin sirrikan da ke cikin waɗannan wasiƙun, ya ɗora mana su yanzu a kan bigiren sabon tsarin taskace tarihi a Najeriya.”
– Toyin Falola, Jami’ar Texas, Amurka.
“Na yi amanna waɗannan wasiƙun sirrin Obasanjo za su samu wurin zaman dindindin a kan dandamalin bajekolin tarihin Najeriya da neman sanin alƙablar da ƙasar nan ta dosa.”
– Cif Emeka Anyaoku, tsohon Sakataren Ƙungiyar Ƙasashe Rainon Ingila (Commonwealth).
Discussion about this post