Rahotanni daga babban birnin tarayyar Najeriya sun nuna cewa ƴan ta’adda ɗauke da zararan makamai sun afka kauyen karamar hukumar Kwali da ke Abuja, inda suka arce da mutane akalla 29.
Wani mazauni. Kauyen mai suna Zubairu Yewuri ya bayyana cewa maharan sun tafi da kanin sa da kuma matan yayyin sa biyu.
Maharan sun ɗauki tsawon awonni uku suna abinda a garin yayin da suka shiga gidaje har guda 8, suka arce da mutum 29.
Wani Daniel Ishaku ya ce, yara da mata ba su kuɓuta daga harin ba domin har da su maharan sun kwashe.
Sunayen wasu daga cikin waɗanda aka sace sun haɗa da Idris Mohammed, Abdullahi Zubairu, Sani S. Magani, Peter Modu, Ibrahim Mamman, Yellow Abdulrasheed, Musa Suleiman, Simbiya Ishaku, Sumaiya Ibrahim, Muktari Yunusa, Mohammed Yeluwa da Rahmat Shagari.
Discussion about this post