Rundunar sojin sama sun kashe ‘yan bindiga da dama a harin bama-baman da jiragen ta suka ka yi wa ƴan bindiga a yankin kananan hukumomin Birnin Gwari, Igabi da Chikun.
Kwamishinan tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya ce gwamnati ta samu labarin haka daga rahoton da rundunar tsaron suka muka wa gwamnati.
Aruwan ya ce an kashe ‘yan bindiga da dama kuma sojoji sun babbake maboyar maharan a dazukan.
Aruwan ya ce rundunar ta Kai wa gidan harsabibin dan bindiga Alhaji Lawan hari sai dai babu tabbacin ko Alhaji Lawan ya mutu a sanadiyyar harin.
“Dakarun sun kuma yi wa maboyar mahara hari a dazukan Kofits da Kuyanbana a karamar hukumar Birnin Gwari.
“Dakarun sun kuma Kona maboyar mahara sannan sun kashe wasu mahara a kauyukan Kuduru da Gonan Baturiya dake da nisan kilomita hudu daga Nabango.
“Yayin da jirgin saman sojojin ke shawagi a yankin Karshi, Kerala da Walawa dake kananan hukumomin Giwa da Igabi dakarun sun hango wasu ‘yan bindiga kuma duk sun kashe su.
Discussion about this post