Gwamnatin Katsina ta haramta siyarwa da busa tabar shisha da sauran muggan kwayoyi a fadin jihar.
Darektan yada labarai na jihar Buhari Mamman-Daura ya sanar da haka a garin Katsina a cikin farkon wannan mako.
Mamman -Daura ya ce hana siyarwa da busa tabar shisha da sauran muggan kwayoyi a jihar na daga cikin dokokin da gwamna Aminu Masari ya saka wa hannu a ranar 5 ga Satumba 2022.
Gwamnati ta saka dokar ne ganin yadda matasa, ƴan mata, magidanta har da matan aure suka maida busa tabar Shisha da shaye shayen muggan kwayoyi suka zama ruwan dare a fadin jihar.
Jami’an kiwon lafiya sun bayyana cewa shisha na illata lafiyar mutum kamar yadda taba sigari ke yi a jikin mai shan ta.
Wadannan cututtuka kuwa sun hada da dajin dake kama huhu, cututtukan dake kama zuciya da sauran su.
Ya ce gwamnati za ta hukunta duk wanda ta kama da laifin karya wannan doka.
Discussion about this post