Rundunar Ƴan sandan jihar Legas ta kama wani matashi mai shekara 25 da ya sace motar mahaifiyar sa daga Ibadan ya kawo ta jihar Legas don ya siyar.
Wannan matashi an gano ko makarantar sakandare bai kammala ba
Kakakin rundunar Benjamin Hundeyin wanda ya sanar da haka wa manema labarai ya ce ƴan sandan dake Ijora Badiya ne suka kama matashin da motar ranar Lahadin makon jiya.
Hundeyin ya ce ‘yan sandan sun kama matashin bayan motar da ya sato din ya tsaya a Ijora Badiya inda ya kira masu jan mota domin a kai motar inda zai siyar.
“Sai dai kafin su tafi mai jan motan ya gano cewa motar ta sace ce inda ya yi gaggawar kiran ƴan sanda.
“Da ya shiga hannun ‘yan sanda matashin ya bayyan cewa ya saci Naira 500,000 daga mahaifiyar sa kuma ya kashe su kaf a caca wanda aka fi sani da Baba Ijebu. Daga baya kuma da ya ga yana buƙatar karin kuɗi don ya sake buga cacakuma babu su shine ya suntumi motar mahaifin fiyar sa ya kawo ta Legas daga n ya siyar ya cigaba da buga harkarsa.
Ya ce rundunar ta kira mahaifiyar wannan matashi domin ta zo ta karbi motarta.
Hundeyin ya ce rundunar za ta tsare matashin a ofishinta har sai ta kammala gudanar da bincike.
Discussion about this post