Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Jigawa Sani Yusuf ya bayyana cewa ambaliyar ruwan sama ya yi ajalin mutum 50 sannan wasu da dama sun rasa gidajen zaman su a jihar Jigawa.
Yusuf ya ce da dama daga cikin wadanda suka rasa gidajen su a dalilin ambaliyan na samun mafaka a gine-ginen gwamnati da sansanoni 11 da gwamnati ta bude a jihar.
Ya ce wasu daga cikin su daga kauyen Balangu suke inda ruwa ya lashe gidaje 237 sannan mutum hudu sun mutu.
Yusuf ya yi kira ga masu zama kusa da kogi da su nemi wurin zama saboda rahotan da NiMet ta fitar ya nuna cewa daminan bana zai yi ruwa mai yawa inda jihohin Arewa za su yi fama da ambaliya mai tsanani.
Discussion about this post