Shirye-shiryen zaɓen 2023 na fuskantar barazanar durƙushewa a jihohi 20, yayin da wa’adin shekaru biyar na aikin aƙalla Kwamishinonin Zaɓe na Tarayya a jihohi 20 ya cika.
Wa’adin 11 daga cikin su ya zo ƙarshe ne tun a ranar 6 Ga Yuli, yayin da sauran 9 kuma su ma ɗin lokacin ritayar sa zai zo cikin wata mai zuwa, Agusta. Dama kuma ɗaya ya ajiye aiki tun cikin watan Afrilu, ya tsunduma siyasa.
Daga cikin waɗanda wa’adin su ya cika, su ka sauka tun farkon Yuli ɗin sun haɗa da: Orji Nkwachukwu (Anambra); Emeka Ononamadu (Enugu); Obo Effanga (Rivers); Chukwuemeka Ezeonu (Imo); Joseph Iloh (Abia) and Mutiu Agboke (Oyo).
Sauran sun haɗa da James Apam (Kogi); Ibrahim Abdullahi (Bauchi); Umar Ibrahim (Gombe) Ahmed Makama (Taraba) da kuma Hussaini Pai (Plateau).
Sai dai kuma in banda Pai, wanda ya yi wa’adin zango biyu, kuma ya kai ƙarshe a yanzu, sauran 10 ɗin duk wa’adin zango ɗaya kowanen su kaɗai ya yi. Wato idan Buhari ya ga dama zai iya ƙara masu wa’adin wasu shekarun kenan.
Haka kuma a ranar 17 Ga Agusta wa’adin wasu Kwamishinonin Zaɓen su takwas zai zo ƙarshe. Sun haɗa da Asmau Maikudi; Riskuwa Shehu; Kassim Geidam (Adamawa); Jibrin Zarewa (Katsina); Abdulganiyu Raji; Samuel Egwu; Mike Igini (Akwa Ibom); da kuma Sadiq Musa (Sokoto).
Daga cikin wannan rukunin da za su sauka a cikin Agusta, akwai waɗanda za su kammala zangon su na biyu ne, waɗanda kenan ba za a iya sake naɗa su ba.
Sun haɗa da Geidam na Adamawa, Zarewa na Katsina, Igini na Akwa Ibom sai kuma Musa na Jihar Sokoto.
Shi kuwa Yilwatda Goshwe na Jihar Benuwai, ajiye aikin INEC ya yi, ya shiga siyasa.
Abin damuwa a nan shi ne yayin da saura watanni shida a yi zaɓen 2023, jihohi kamar 20 sun kusa kasancewa ba su da Kwamishinonin Zaɓe na Tarayya, lamarin da zai iya kawo wa zaɓen 2023 tangarɗa.
Daga cikin ayyukan zaɓen da zai fara samun cikas, akwai batun amincewa da wasu buƙatu na aikin ci gaba da rajistar masu neman mallakar katin zaɓe (CVR), wanda aiki ne na Kwamishinan Zaɓe na Tarayya (REC).
Ya kamata a ce tuni har an naɗa sabbin da za su maye gurabun waɗanda wa’adin su ya cika, har ma da na waɗanda wa’adin su bai cika ba, tun kafin lokacin cikar wa’adin kowanen su ya yi.
Amma har yanzu Shugaba Muhammadu Buhari bai yi komai a kai ba, duk kuwa da cewa ko da ya fitar da sunayen sabbin, sai ya aika Majalisar Dattawa ta tantance su tukunna, kafin su fara aiki.
Discussion about this post