Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani magidanci mai suna Ojo Babatunde da ya rika lalata da agola a gidansa ƴar shekara 15.
Kakakin rundunar Sunday Abutu ya tabbatar da haka wa manema labarai a garin Ado-Ekiti ranar Laraba.
Abutu ya ce ƴan sandan sun kama Babatunde a gidansa dake lamba 15 layin Edugbe dake unguwar Obadore a kauyen Omuo-Ekiti dake karamar hukumar Ekiti ta Gabas.
“Yarinyar dake dauke da cikin wata hudu ta tabbatar cewa Babatunde wanda shine mijin mahaifiyar ta ne ya dirka mata ciki.
“Ta ce Babatunde ya fara danne ta a lokacin da mahaifiyarta da je asibiti haihuwa inda aka samu matsala aka kwantar da ita har tsawon makonni uku a asibiti.
“Ta ce a wannan lokaci Babatunde ya mai da ita tamkar matarsa inda yake lallabarta zuwa gona yana danne ta. Ta ce da zarar ya kammala zai ja kunnenta da idan ta faɗi zai kashe ta.
Abutu ya ce da Babatunde ya shiga hannu ya tabbatar wa jami’an tsaron cewa shine ya dirka wa yarinyar ciki.
Ya ce Babatunde ya nemi afuwa inda ya ce ya aikata haka ne saboda bin hudubar shaidan da yayi.
Abutu ya ce za a kai Babatunde kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike domin yanke masa hukunci.
Discussion about this post