A ranar Litinin din makon jiya ne wani magidanci mai suna Surajo Mansur ya roki kotun shari’a dake jihar Kaduna da ta raba auren sa da matarsa Bilkisu Muhammad kowa ya huta tunda har zata iya kaishi kotu.
Mansur wanda kannensa Sulaiman ya wakilta a kotun ya ce yana so a raba auren ne saboda maka shi a kotu da matarsa ta yi.
Bilkisu ta kai karar mijinta amma kuma ta take rokon kotu da kada ta raba auren su har sai mijinta ya biya bukatun su.
Ta kara da cewa Mandur ya tafi Legas ya yi zaman sa can ba ya ba su abinci suna cikin yunwa, rashin wurin zama da dai sura su.
Ta ce a yanzu haka basu da wurin zama, babu abinci sannan har yanzu ba a biya kudin makarantar yara ba.
Bilkisu ta roki kotu da ta tilasta Mansur ya riƙa biyan buƙatun iyalinsa.
Mansur ya ce ya yi kokarin biyan kudin hayan dakin da iyalinsa ke zama amma mai gidan hayan ya ki karban kudi cewa ya bada dakin wa wani.
“Sannan ‘ya’yan mu dake makaranta na rubuta jarabawa zan biya kudin makarantar su bayan sun kammala rubuta jarabawar.
Alkalin kotun Malam Rilwanu Kyaudai ya umurci Mansur da ya biya duk bukatun iyalinsa sannan ya kawo mai gidan hayan da iyalinsa ke zama a zaman da kotun za ta yi nan gaba.
Kyaudai ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 21 ga Yuni.
Discussion about this post