Sanata Adamu Aliero ya bayyana komawarsa PDP daga Jam’iyyar APC.
A sanarwar da yayi ranar Alhamis, Aliero ya ce rashin jituwa tsakanin sa da jam’iyyar a jihar ya sa dole ya hakura da jam’iyyar ya koma PDP.
Idan ba a manta ba Jam’iyyar APC ƙarkashin gwamna Abubakar Bagudu ta wancakalar da ɗan takarar gwamnan jihar sanata Abdullahi wanda ke ɓangaren Aliero.
Aliero ya ce ” Na gaji da zaman takaici a APC, ba zan iya cigaba da ɗaukan wulaƙanci, wariya da iko da ake nuna min da magoya baya na ba. A dalilin haka na hakura da jam’iyyar.