Ɗan gwamnan jihar Kaduna Brllo El-Rufai ya yi nasara a zaɓen fidda gwani wanda aka yi a garin Kaduna ranar Juma’a.
Bello wanda shine kusan ɗan takara tilo wanda yake neman kujerar a jam’iyyar APC ya sha alwashin kawo cigaban da ba a taba samun irinsa ba a shiyyar Kaduna ta Arewa.
Da yake bayyana farin cikinsa a shafin sa ta tiwita, Bello ya ce ” Ba zan ba ku kunya ba a majalisa, zan tabbata Kaduna ta Arewa ta fi yadda take a yanzu ta hanyar samar da kyakkyawar wakilci da kwararo cigaba da ingata jin daɗin mutanen Kaduna ta Arewa.
Ya yabawa wakilai da suka zaɓe shi sannan ya yi kira da azo a haɗa hannu gabaɗayi ayi aiki domin samun nasara a babban zaɓe da ke tafe a shekara mai zuwa.