Gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya bayyana cewa gwamnatin sa zata kirkiro sabbin gundumomi 268, Sabbin masarautu biyu kuma zata dawo da masarautu uku da aka dakatar a jihar.
Gwamna Lalong ya kuma ce gwamnati ta Kara wa wasu masarautu biyar a jihar girma.
Kakakinngwamna Lalong wanda shine ya fitar da sanarwar ya kasafta yadda gwamnati ya ta kirkiro gundumomin daya bayan daya a kamar haka Barkin Ladi 17, Bassa 19; Bokkos 17, Jos ta Gabas 10, Jos ta Arewa 15, Jos ta Kudu 14 Kanam 20 da Kanke 11.
Saura kuwa sune Langtang ta Arewa 16, Langtang ta Kudu 7, Mangu 22, Mikang 10, Pankshin 23, Qua’an Pan 16, Riyom 12, Shendam 22 da Wase 17”.
Masarautun da za a dawo da su sun hada da Da-Gwom Rwei dake Barkin Ladi, Da-Gwom Rwei (Gyel) dake Jos ta Kudu da Da-Gwom Rwei (Riyom) dake Riyom.
Sannan masarautun da za a kara wa girma sun hada da Rwei Kabong dake karamar hukumar Jos ta Arewa, Gwom Rwei Zawan dake Jos ta Kudu, Ponzhi Bwarat dake Langtang ta Arewa, Ponzhi Gani (Sa) da Ponzhi Tumwat duk a Langtang ta Arewa.
Ya ce ofishin sakataren gwamnati za ta bada sunayen Sabin dagatan da aka nada nan ba da dadewa ba.
A karshe gwamna Lalong ya yi ƙarin haske game da maƙasudin ƙirƙiro waɗannan gundumomi ya na mai cewa gwamnati ta yi haka ne domin ta kai cigaba kusa da mutane a jihar.
Discussion about this post