Sanata Uba Sani dake wakiltar Kaduna Ta Tsakiya a majalisar dattawa ya sayi form din takarar gwamnan jihar Kaduna ranar Alhamis.
Tawagar sanata Uba ta dira ofishin jam’iyyar APC dake Abuja inda daya daga cikin shuagabnnin jam’iyyar Suleiman Argungu ya ƙarɓe su.
Bayan ya sayi fom ɗin, sanata Uba ya gana da manema labarai a kafin ya koma gida ya huta
” Yau dai ya tabbata na shiga takarar gwamnan jihar Kaduna. Gani a nan tare da magoya baya mun sayi fom.
” Babban buri na shine in zama gwamnan jihar Kaduna domin cigaba da kyawawan ayyukan da gwamna mai ci, Nasir El-Rufai ya aiwatar, Gwamnan da ba a taba yin irinsa ba a jihar, sannan kuma inngina daga nan domin mutanen mu da cigaban jihar mu.
Haka kuma shima ɗan takarar gwamnan jihar Honarabun Sani Shaaban ya sayi fom din yin takarar.
Saidai kuma ba da kanshi ya sayi fom ɗin ba, ƴaƴan sa ne su 17 suka tara kuɗi suka siya masa fom din takarar.