A wajen taron bada kyautattuka na Oscar da aka yi a Amurka ranar Lahadi, shahararren mai barkwanci kuma wanda ya ke gabatar da taron ya sha lafiyayyar mari daga wanda ya ci kyautar babban jarimi a harkar finafinan na shekara.
Will Smith da ke aure da Jada Pinket ya tashi takanas ta kano kamar zai je ya tambayi Chris Rock wanda ke gabatar da taron ya gaura masa mari saboda yayi barkwanci da sunan matar sa.
Will Smith ya fusata bayan Chris Rock ya ambaci sunan Jada Pinket sannan ya yi barkwanci da rashin gashin da ke kanta wand cuta ce take fama da shi.
Bayan Smith ya gaura masa mari ya koma kujerar sa ya zauna sannan ya gargaɗe sa kada ya kuskura ya sake ambaton sunan matan sa a barkwancin sa.
Shi ko Rock da ya ke kwararre ne, ya bayyana cewa bai yi haka don ya tozarta matan Smith ba, barkwanci ne kawai.
” Kai lallai na sha marin gaske yau, amma barkwanci ne ban yi dhi da nufin in tozarta ta ba ko kuma in ci mutuncin Pinket.
A karshe, Smith bayyana a yi masa hakuri bisa abinda ya aikata a bainar jama’a. Sannan ya godewa masu shiyar bikin Oscar bisa karrama shi da kyauta jarimin jarimai na wannan shekara.