[youtube https://www.youtube.com/watch?v=hU_OwgHzJrg&w=760&h=365]
Kungiyar matan gwamnonin Najeriya NGWF ta tabbatar da bidiyon da ya karaɗe kafafen sada zumunta dake nuna ziyartar uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari da suka yi a Dubai domin ta ya ta murnar zagayowar ranar haihuwarta.
Sai dai kungiyar ta bayyana cewa ba murnan zagayowar ranar haihuwar ba ce kawai ya kai su kasar Dubai.
A ranar Laraba shugaban kungiyar kuma uwargidan gwamnan jihar Ekiti Bisi Fayemi ta sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai.
Bisi ta ce murnar zagayowar ranar haihuwar Aisha Buhari ya zo a lokacin da matan gwamnonin Najeriya suka yi tafiya zuwa kasar Dubai domin yin wani aiki ta musamman.
A bidiyon wanda ƴan Najeriya suka koka da shi an ga Bisi dauke da ‘Kek’ a kwali inda ta jagoranci sauran matan gwamnonin domin mika wa Aisha a wannan rana da ta cika shekaru 51 a duniya.
A jawabin da suka yi ranar Laraba matan gwamnonin sun ce yin wannan tafiya zuwa Dubai da suka yi dole ne. Haka ita ma ziyartar da suka kai wa Aisha Buhari din.