Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a kwashi dala miliyan 8.5 domin a kashe su wajen jigilar ‘yan Najeriya aƙalla 5,000 da ke Ukraniya.
Waɗanda za a kwaso ɗin dai su na maƙale ne a can sun rasa hanyar dawowa, tun bayan da yaƙi ya ɓarke tsakanin Rasha da Ukraniya a ranar 21 Ga Fabrairu.
Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya ya ce yawancin ‘yan Najeriya mazauna Ukraniya sun gudu, sun tsallaka cikin ƙasar Poland, Romaniya, Hungary da Slovakia.
Ƙaramin Ministan Harkokin Ƙasashen Waje Zubairu Dada, tare da Ministar Ayyukan Jinƙai da Agaji, ne su ka bayyana haka a Fadar Shugaban Ƙasa, a ƙarshen taron Majalisar Zartaswa da aka gudanar a ranar Laraba.
Matakimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ne ya jagoranci taron na ranar Laraba, a Babban Ɗakin Taron Majalisar Zartaswa da ke Fadar Shugaban Ƙasa.
Karamin Ministan Harkokin Waje Dada ya ce an sa hannun amincewa a fidda kuɗaɗen ne bayan da Ma’aikatar Harkokin Waje da Ma’aikatar Ayyukan Jinƙai, Agaji su ka rubuta wasiƙar bai-ɗaya tare ta abin da za’a kashe wajen dawo da ‘yan Najeriya ɗin zuwa gida Najeriya.
Ya ce Kamfanin Zirga-zirgar Jiragen Sama na Air Peace ne aka tuntuɓa domin ya samar da jirage uku waɗanda za su riƙa jigila ba dare ba rana, kuma ba ƙaƙƙautawa har sai an kwaso su da gaggawa.
Minista ya ce adadin waɗanda za’a kwaso ɗin akwai 940 a Romaniya, 150 daga Slovakia, 350 daga Poland, waɗanda su ka rigaya su ka yi rajistar son dawowa Najeriya.
Ya ce Ma’aikatar Ayyukan Jinƙai da Agaji ce ta rubuta takardar buƙatar waɗannan kuɗaɗen domin a yi aikin kwaso yan Najeriya ɗin.
“Kuɗin da aka nema dala miliyan 8.5 kuma nan take Shugaba Muhammadu Buhari ya amince.
“Kuma ya kamata a fahimci cewa ba a biyan kuɗin tikitin jirgi kawai za a kashe kuɗaɗen ba. Kuma ai za a yi ɗaukar nauyin kula da waɗanda su ka zaɓi tsayawa can ƙasashen, kafin ƙura ta lafa su koma.”
Discussion about this post