Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna Sule Hunkuyi ya fice daga jam’iyyar PDP.
Idan ba a manta ba, sanata Hunkuyi ya koma jam’iyyar PDP ne ana gab da zaɓen 2019 bayan sun raba jiha tsakanin sa da gwamna Nasir El-Rufai.
Rashin jituwar ta su ta yi munin da hatta wani gidansa sai da gwamnatin Kaduna ta rusa a wancan lokacin.
Bayan haka sai ya fito takarar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar PDP amma kuma a nan ma hakar sa bai cimma ruwa ba domin tun a zaɓen fidda ɗan takara Honarabul Isah Ashiru ya wancakalar da shi da wasu ƴan takaran da suka fafata wurin neman kujerar gwamnan jihar.
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Tanko Wusono ya tabbatar da wasikar ficewar sa daga PDP ra ar Alhamis a Kaduna.
” Muna mishi fatan Alkhairi, ba wannan ne karon farko da ya fice daga jam’iyyar ba ya kuma dawo da kansa. Mu dai mun sani ficewar sa ba zai yi wa jam’iyyar PDP komai ba.
Wani mazaunin Kaduna da ya zanta da PREMIUM TIMES HAUSA ya ce mutanen Kaduna ba su yi mamakin canja shekar Hunkuyi ba.
“Mutanen Kaduna ba za su iya faɗin ko sau nawa bane Hunkuyi ya canja jam’iyya tun daga 1999. Yau ka ji a nan idan bai samu yadda yake so ba sai kaji a can.
” Shi dai gwamna ya ke so idan ya ga ba zai samu ba sai ya waske. Tun ƴan siyasa na ganin shi wani abu ne yanzu ba su ganin shi wani da zai iya yin tasirin arziki a siyasar Kaduna.
Sai dai kuma a hasashen wani mazaunin Kaduna shima, Tanimu Hamisu ya ce akwai yiwuwar Hunkuyi za su gyaro ta ne da gwamnan jihar Kaduna El-Rufai su yi aiki tare a zaɓen 2023 domin akwai babban aiki a gaba.
Discussion about this post