Ƙungiyar Tsoffin Ɗaliban Jami’ar Fasaha ta Tarraya, Owerri (FUTA) sun bayyana cewa matsayin farfesan da jami’ar ta bai wa Ministan Fasahar Zamani, Isa Pantami, ba ta face ba, domin ba a bi ƙa’idar cancanta wajen ba shi matsayin ba.
Wannan matsaya ta su na cikin wata takardar da Shugaban Ƙungiya na Ƙasa, Ndubuisi Chijioke ya sa wa hannu, tare da sa hannun Sakataren Ƙungiya, Kingsley Azuaru.
Ƙungiyar tsoffin ɗaliban ta ce ita ƙin amincewa da digirin-digirgir na farfesa da FUTO ta naɗa wa Pantami, daidai ne da ASUU ta yi haka nan.
Sun ce ASUU ta yi daidai da ya shawarci FUTO cewa ta janye matsayin farfesan da ta bai wa Pantami.
“Mu tsoffin ɗaliban FUTO mun ƙara nanata matsayin mu cewa farfesan da aka bai wa Minista Isa Pantami, bai dace ba.
“Kuma mu tsoffin ɗaliban FUTO mun ji daɗi tare murna da jinjina ga Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) su ka ƙi amincewa da digirin-digirgir ɗin da FUTO ta bai wa Pantami. Don haka mu na ƙara jaddada cewa farfesan da aka bai wa Minista Pantami kawai harƙalla ce kawai.”
Sun ce abin takaici ne cewa wasu dattawan tsoffin ɗaliban FUTO za su gayyaci shugabannin FUTO, domin yin yin walimar murna da goyon bayan matsayin farfesan da aka bai wa Pantami.
A kan haka ne ƙungiyar ta ce ita ma ƙungiyar ta dattawan tsoffin ɗaliban FUTO, ba halastacciyar ƙungiya ba ne a bisa tsarin dokokin Najeriya.
“Yaudara kawai Kungiyar Dattawan Tsoffin Ɗaliban FUTO ke yi domin su cuci jama’a, ganin yadda Jami’ar FOTO ta haɗa hannu tare da tsoffin ɗaliban dattawa har su ke ƙoƙarin shirya taron goyon bayan Pantami.
Premium Times Hausa ta buga labarin yadda Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta ce digirin-digirgir ɗin Minista Pantami na ‘Jami’ar Jatau Na Albarkawa’ ne.
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) sun yanke hukunci tare da ɗaukar matsayin cewa Digirin-digirgir na Farfesan da aka ba Ministan Sadarwar Zamani, Isa Pantami, haramtacce ne, don haka ba su yarda da shi ba.
Sun bayyana hakan ne bayan tashi daga taron su na tsawon kwanaki biyu da suka gudanar a Jami’ar Legas.
Majalisar Zartaswar ASUU ta ce ta bi diddigin yadda Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri (FUTO) ta bayar da muƙamin Farfesan Nazarin Kare Aikata Laifuka a Kafafen Sadarwar Zamani (Cyber security) cewa an kauce wa ƙa’ida da matakan da suka kamata ya bi kafin ya kai ga matsayin.
Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, Emmanuel Osodeke, ya ce:
“Majalisar Zartaswar ASUU ta yi Allah-wadai da matsayin ‘Farfesan’ da aka bai wa Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami.
“Daga hujjojin da muka tattara kuma muka tabbatar, Dakta Pantami bai cancanci muƙamin Farfesa ba. Sannan kuma ba shi matsayin ya kauce wa tsari, matakai da ƙa’idojin da ya kamata ya bi kafin ya zama farfesa. Kuma kowa ko a wace jami’a ce, sai ya bi waɗannan hanyoyi da matakai sannan ya ke zama farfesa a jami’a.
“Majalisar Zartaswar ASUU na kira ga dukkan mambobin ta da sauran rassan ƙungiyar na faɗin ƙasar nan, kada su amince kuma kada su riƙa bai wa Pantami girman da ake bai wa Farfesa.”
ASUU ta ce matsayin da ta ɗauka a yanzu ƙarin jaddadawa ce kan matsayin ta na farko da ta ɗauka cikin 2021.
Daga nan ta ce dukkan mambobin ta da su ke da hannu wajen cuku-cukun bai wa Pantami matsayin farfesa, za a hukunta su, don na baya su ɗauki darasi.
Discussion about this post