Ko wata ɗaya dindi ba a cika ba bayan da sojojin Najeriya su ka fatattaki ‘yan bindiga a dajin Ganɗo cikin Ƙaramar Hukumar Bukkuyum, mazauna yankuna biyu sai da suka biya ‘yan bindiga Naira miliyan 12, kafin su karɓo fansar mutanen su 26 da ke hannun ‘yan bindiga a cikin dajin.
Waɗannan garuruwa kuwa su ne Gana da Nasarawar Burkullu.
Ganɗo surƙuƙin daji ne da ke ƙarshen Gwashi da mutanen kewaye da garin. Wuri ne da ‘yan bindiga ke amfani da shi a matsayin maɓuyar su kuma daga can su ke nausawa su je kai hare-hare a Anka, Bukkuyum da wasu sassan Jihar Kebbi.
PREMIUM TIMES ta buga yadda sojoji suka kutsa dajin, su ka fatattaki mahara, kuma su ka ceto mutane da dama, har da dabbobi masu yawa.
Wani ɗan ƙauyen Gwashi mai suna Ayuba Mohammed, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa mazauna yankin na farin ciki ganin irin yadda sojoji suka samu nasara kan ‘yan bindiga.
‘Mun Biya Naira Miliyan 12 Kafin A Sako Mutanen Mu’:
Wasu mazauna yankunan sun yi wayar tarho da wakilin mu cewa sai da suka biya zunzurutun kuɗi har naira miliyan 12 tukunna sannan aka sako masu mutum 26.
“Mutum 14 ‘yan ƙauyen Gana ne, 12 kuma daga Nasarawar Burkullu aka kama su.
“Mutanen Gana sun harhaɗa naira miliyan 7, su kuma ‘yan Nasarawar Burkullu suka biya naira miliyan 5.”
Wani basaraken gargajiya kuma Hakimin Zugu, ya nemi a ɓoye sunan sa, amma ya ce su yanzu a yankunan na su har biyan harajin zama lafiya da ‘yan bindiga ya zame masu jiki.
“Ko kwanan nan sun ɗora wa ƙauyukan mu 9 harajin zaman lafiya. Ai ina jin mun yi maganar da ke kwanan baya ko?
“Batun kuɗaɗen da mutanen Gana da Nasarawar Burkullu suka haɗa wa ‘yan bindiga suka karɓo mutum 26, gaskiya ce. Saboda wasu sarakunan gargajiya ma sun shaida min cewa sun bayar da ta su gudummawar kuɗaɗen, don dai a ceto mutanen daga hannun masu garkuwa.”
Sai dai ya ce farmakin da sojoji su ka kai wa ‘yan bindiga ya rage masu ƙaimi sosai. Amma fa har yanzu akwai sauran mutane a hannun ‘yan bindiga a cikin dajin.
Mutane da yawa da wannan jarida ta yi hira da su daga yankin, duk sun tabbatar mata da an biya kuɗaɗen.
Wani mai suna Abdullahi Musa ya ce a ƙauyen Gana, ‘yan bindiga sun yanka haraji daidai ƙarfin mutum. Hai hali harajin sa daban da na talaka.
“Kuma ko ba a kama wani naka an tsare ba, sai ka biya harajin. Domin ba a kama kowa a gidan mu ba, amma sai da muka biya naira 50,000.”
PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Zamfara, Mohammed Shehu. Sai ya ce ba zai yi magana ba tukunna, har sai ya tabbatar da an biya kuɗaɗen. Domin labarin bai je masu ba.
Discussion about this post