A wani rahoto wanda Jaridar Daily Trust ta buga ta bayyana cewa duk da babu sahihin kundin bayanai dake bada kididdigar yawan sakin aure da ake yi, an yi rajistar akalla rabuwar aure sama da miliyan 1.7 a jihar Kano kamar yadda darektan Muryar Zawarawa ta jihar Altine Abdullahi ta bayyana.
Wakiliyar PREMIUM TIMES Titilope Fadare ta yi tattaki na musamman zuwa wasu yankunan Abuja inda ta tattauna da mata da suka rabu ba mazajen su da kuma yadda sake ya zama ruwan dare a wadannan yankuna.
Yadda na haifi ‘Ya ta ina kwashe kaya na cikin dare bayan mijina ya sake ni a Abuja
” Na hadu da mijina Salisu a Kasuwar Gosa, Mpape a Abuja” , inji Halima ” Sai dai kash, soyayyar da muka murza kamar za mu hadiye juna bai dore ba bayan mun yi aure. Kafin mu yi aure muna tare kullum muna hirar yadda za mu soye juna idan muka yi aure.
Halima ta ce mahaifiyar Salisu ba ta so wannan aure na su ba tun kafin su yi auren amma kuma ta tirje tana fatan idan suka yi aure za su samu daidaituwa mahaifiyar mijinta.
Abin bai yiwu ba bayan sun haifi da daya Salisu ya banka mata saki uku a lokacin tana da cikin wata tara.
” Ranar da da ya mika min takardar saki na fara nakuda domin cikin a ya tsufa. Ya zo cikin dare ya mika min saki sannan ya umarce ni in gaggauta tattara nawainawa in fice masa daga gida. Cikin wannan dare haka na rika kwaso kaya na ina saka sau cikin jaka. Ina cikin wannnan hali ne haihuwa ya zo min. Ba ni da waya babu kowa gidan haka na rika juyi har da ya fito.
” Na yanke cibin jaririn na yi mata wanka sannan na fice daga gidan sa na koma gidan Iyaye na a Berger.
Halima ta ce tuni ta cigaba da rayuwarta har ta samu wani saurayin da yake sonta da aure yanzu haka a Abuja kuma suna shirin su yi aure.
Mata da dama da aka tattauna da su daga wasu jihohin sun bayyana yadda mazajensu suka maida zawarawan dole. Wasu da ‘ya’ya amma suka sake su suka kama gabansu.
Malaman addini da aka tattauna da su sun bayyana cewa mazaje ba su yi wa ka da sharadin saki a addinin musulunci. Duk yadda abin ya zo musu haka suke yi ba su duba umarnin da Allah ya bada da yadda musulunci ta shardanta.