Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya bayyana cewa shekara shida bayan an kafa asusun BHCPF ‘yan Najeriya basu fara cin moriyar kudaden ba.
Mustapha ya ce gwamnati ta kafa wannan asusu domin samar wa kowa da kowa kiwon lafiya ta gari a fara shi mai sauki
Sai dai tun da aka kafa asusun ‘yan Najeriya basa samun lafiya ta gari sannan koda sun samu din za su same shi ne da tsada.
Sakataren gwamnatin tarayya ya fadi haka ne a taron nada kwamitin mutum 15 domin ido a asusun BHCPF da aka yi a Abuja ranar Talata.
Menene asusun BHCPF
Basic Health Care Provision Fund (BHCPF) ya samo asali ne a shekaran 2014 inda gwamnatocin kasashen Afrika suka amince su ware kashi daya daga cikin kudin kasafin kudaden su na duk shekara domin inganta fannin kiwon lafiyar mutanen kasashen su.
A shekaran 2018 ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya saka hannu a kan dokar fara aiki a Najeriya.
A kasafin kudin shekarar 2022 gwamnati ta ware Naira biliyan 54 wa asusun BHCPF
Sabon kwamiti
Gwamnati ta kafa wannan kwamiti ne domin ganin an yi amfani da kudaden dake asusun BHCPF domin samar wa mutanen kasa kiwon lafiya a farashi mai sauki.
Wannan karo gwamnati ta ce za ta hada hannu da masu ruwa da tsaki a fannin lafiya domin tsara hanyoyin da za su taimaka wajen ganin an kai ga cin nasara.
Discussion about this post