Ƙoƙarin da wasu mambobin Majalisar Tarayya ke yi, domin neman halasta noman wiwi da kuma amfani da ita wajen maganin cututtuka ya ci tura, saboda kwamiti ya yi fatali da bukatar.
A ranar Laraba ce dai Kwamitin Majalisar Tarayya mai lura da Muggan Ƙwayoyi ta bayyana cewa ba zai taɓa amincewa kudirin ya samu karɓuwa har a amince da shi ba.
Shugaban Kwamiti Francis Agbor, ya ce irin yadda taba wiwi ta zama sanadin aikata muggan laifuka a ƙasar nan, idan aka halasta noman ta, muggan laifuka za su ƙaru sosai a ƙasa.
Honorabul Meriam Onuoha ce ‘yar APC daga Imo ta gabatar da kudirin, inda ta nemi a halasta noman wi domin a riƙa amfani da ita wajen warkas da marasa lafiya.
Yayin da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisa, Ado Doguwa daga Kano ya nemi a tsaurara hukunci a kan manyan dillalan wiwi da masu saye su na sayarwa da masu tu’ammali da ita, shi kuwa Kakakin Yaɗa Labarai na Majalisar Tarayya, Honorabul Ben Kalu, ya nemi a halasta noma da shan taba wiwi.
Da ya ke bayani, Shugaban Hukumar NDLEA, Buba Marwa ya nemi a sayi jiragen ruwa ƙanana domin a raba wa jami’an NDLEA, waɗanda Marwa ya ce za su riƙa sintirin hana shigowa da masu sumogal ta ƙananan jiragen ruwa.
Discussion about this post