Rundunar ƴan sandan Katsina ta gabatar da wani matashin yaro mai shekaru 14 kuma ɗan bindiga.
Da yake gabatar da wannan ƴaro tare da wasu ƴan bindigan 19, kakakin rundunar ƴan sandan ya ce wannan ɗan yaro ya iya sarrafa bindiga AK47.
” Wannan ɗan yaro ya ce da shi ake kai hare-hare ƙauyuka a jihar Katsina da ma wajen jihar. Ya ce ya samu horon iya kai hare-hare, satar shanu da yin garkuwa da mutane daga gogarman daji, Maliki. Ya kara da cewa zai iya tunawa ya kashe wasu mutane biyu a ƙauyen Mallamawa.
” Da shi aka kai harin Dankulumbo da Kukar Babangida, a karamar hukumar Jibiya. Sannan kuma ya ce ba zai iya tuna yawan dabbobin da ya sace ba, da kuma yawan ƙauyukan da aka kaiwa hari da shi.
A karshe dai wannan matashin ɗan bindiga ya ce ya yi nadamar abin da ya aikata a baya.
Sauran waɗanda aka kama aka kuma gabatar da a gaban ƴan jaridasuna haɗa da Sama’ila Rabiu da aka kama shi da shanu 56, jaki ɗaya da Akuya 3.
Sai kuma Garba Isa, Kabir Garba da Yusuf Garba su kuma su ke siyo musu mai, ajiya da karbar kuɗi da kuma saida musu da dabbobin da suka sace.
Jihar Katsina na daga cikin jihohin da suke fama da ayyukan ta’addanci a yankin Arewa Maso Yamma.
Akwai wasu ƙananan hukumomi 13 da aka datse hanyoyin sadarwa daga can.
Discussion about this post