Gwamantin Tarayya ta bayyana cewa ta bankaɗo alaƙar da ke tsakanin gogarman neman kafa ƙasar Yarabawa zalla, Sunday Igboho da kuma ƙasurgumin mai ɗaukar nauyin ‘yan ta’addar Boko Haram.
Ministan Shari’a Abubakar Malami ne a bayyana wa taron manema labarai haka a Abuja a ranar Juma’a, inda ya yi masu ƙarin haske kan ayyukan zagon ƙasa da cin amanar ƙasa waɗanda Sunday Igboho da Shugaban Biafra, Nnamdi Kanu su ke yi wa Najeriya da gwamnatin ƙasar.
“Bincike ya nuna cewa kamfanin Adeyemo, mallakar Sunday Adeyemo (Igboho) ya tura wa wani mai suna Abdullahi Usman kuɗi har Naira miliyan 12.75.
“Ana zargin Usman da ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci a Najeriya.
Igboho ya aika masa da kuɗaɗen ta ƙarƙashin kamfanin sa Adeosun International Concept Ltd, har naira miliyan 12,75,000. Ya aika da kuɗaɗen ne ga Abdullahi Umar Usman ta hannun kamfanin Abbal Baƙo & Sons.
“Mun kuma gano akwai alaƙa tsakanin SURAJO ABUBAKAR MUHAMMAD, wanda a yanzu haka ke zaman wa’adin ɗaurin rai-da-rai a kurkukun Dubai, saboda a ƙasar Dubai ɗin an kama shi da laifin ɗaukar nauyin Boko Haram a Najeriya.
“Hakan ya nuna akwai alaƙa tsakanin ‘yan Boko Haram da Sunday Igboho, wanda shi ma yanzu haka ke tsare a kurkukun Kwatano, babban birnin ƙasar Jamhuriyar Benin.”
Minista Malami ya ƙara cewa bincike ya bankaɗo yadda Sunday ke da alaƙa da asusun ajiya a banki har asusu 43 a cikin bankuna guda 9.
Malami ya bayyana yadda aka riƙa saƙala-saƙalar kuɗaɗe a asusun da kuma Igboho da waɗanda su ka tabbatar da alaƙar sa da masu ɗaukar nauyin ta’addanci.
Discussion about this post