A hira da PREMIUM TIMES HAUSA ta yi da wani likita, Sunday Ateboh, ya godewa gwamnatin tarayya a madadin iyaye maza kan hutun haihuwa da gwamnati ta bada idan matayen su sun haihu.
Idan ba a manta ba gwamnatin tarayya ta sanar da baiwa iyaye maza hutun makonni biyu idan matayen su suka haihu.
” Wannan abu yayi kyaun gaske, domin kuwa babu iyaye maza na bukatar a basu irin wannan hutu domin su koma ga matayen su dake jego su taya su dawainiya. Sai dai kuma abin da gwamnati ba ta yi shine ta dan basu tuici, domin hidimomin da za su yi a wannan lokaci.
Kalli Bidiyo:
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=nW1FJWEX32w&w=760&h=388]