Kwamishinan ƴan sandan jihar Zamfara Ayuba Elkanah ya bayyana wa manema labarai cewa dakarun ƴan sanda sun kama kasurgumin ɗan bindiga kuma nagaban goshin gogarman ƴan bindiga Turji.
A wannan ganawa da Elkanah yayi ya taso keyar Bello Rugga tare da wasu kwamandojin sa da masu yi musu leƙan asiri 21 a garin Gusau, jihar Zamfara.
” Ranar 1 ga Oktoba, jami’an mu bayan samun wasu bayanan sirri, suka kai farmaki karamar hukumar Gumi da kauyuka Gidan Bita, Malakar da dajin Kagara, kuma Allah ya basu sa’an kama ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Rugga da wasu maƙarraban sa.
Elkanah ya kara da cewa Bello Rugga ne babban kwamandan gogarman ƴan ta’adda Turji wanda ya bashi cikakken ikon aikata ta’addanci a dazukan dake yankin karamar hukumar Gumi tare da wasu kwamandojin sa.
Rugga yayi ƙaurin suna wajen kai hare-hare a garuruwan jihar da yin garkuwa da mutane a yankunan da ke kewaye da Zamfara.
” Bayan ƴan bindigan da aka kama, an ƴan sanda sun kama wasu ƴan gari da ke aiki da ƴan bindiga. Mun kama su a daidai suna kokarin kaiwa ƴan bindigan muggan kwayoyi, ganyen wiwi da jarkunan fetur.
Sannan kuma an kwato makamai masu yawa.
A karshe Elkanah ya ce jami’ai za su ci gaba da farautar ƴan bindigan har sai an ga bayan su.
Discussion about this post