Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bashi alheri ne, domin da kudaden bashi Najeriya ta fita daga matsin tattalin arzikin da ta afka sau biyu a baya.
Ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabin kasafin 2022 a Zauren Majalisa, a ranar Alhamis. Ya ce bashi ne ya rufa wa Najeriya asiri ta tsallake siraɗin matsin tattalin arzikin ƙasa sau biyu.
Ya ce ba don tulin basussukan da aka shiga ba, da har yanzu ƙasar nan na fama da matsin tattalin arziki.
Sai dai kuma duk da bugun ƙirjin da Gwamnatin Buhari ke yi na fita daga matsin tattalin arziki, ƙididdigar NBS ta nuna akwai matalauta masu fama da ƙuncin rayuwa sama da miliyan 84 a Najeriya, ƙasa mai yawan al’umma miliyan 220.
Sannan kuma har yau kusan shekaru biyu amfanin gona da sauran kayan abinci da kayan masarufi sai tashi su ke yi.
Ita kan ta gwamnatin sai shelar alwashin fitar da mutum miliyan 100 ta ke yi, wanda ta ce za ta yi cikin shekaru 10.