Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya tsinewa ƴan bindiga da masu ɗaukar nauyin su a ƙasar nan.
Waɗannan na daga cikin kalaman gwamna El-Rufai a lokacin da yake jawabi ga ƴan jihar a tattaunawa da yayi da tashoshin radiyo na jihar a fadar gwamnatin jihar ranar Talata.
El-Rufai ya ce za a toshe layukan sadarwar wasu kananan hukumomi da ƴan bindiga suka tsananta kai hare-hare da zarar jami’an tsaro sun buƙaci a yi haka.
Bayan kammala wannan tattaunawa da yayi da jawabi ga ƴan jihar ranar Talata, kwamishinan tsaron jihar ya yi ganawa da ƴan jarida ranar Laraba inda ya bayyana sabbin matakan da gwamnati ta ɗauka bayan toshe hanyoyin sadarwar jihar.
Ga tattaunawar
Gwamnatin Kaduna ta sanar da dakatar da kabukabun acaba daga ranar Laraba, 29 ga Satumba, ba za su sake fita aiki ba sai kuma wada Allah yayi.
Hakan da wasu dokoki na kunshe ne a doguwar jawabi da kwamishinan tsaron jihar Kaf na yayi ranar Laraba a Kaduna.
A cikin jawabin Samuel Aruwan ya ambato wasu matakai da gwamnati ta dauka bayan hana ƴannacaban da aka yai kamar haka:
– Duk wanda aka kama dauke kowani irin makami zai ɗanɗana kuɗar sa.
– Ƴan Keke-Napep za su rika aiki ne daga karfe 7 na safe zuwa shida na yamma, idan ka kuskure su kuma sai ka tako zuwa gida.
– Duka motocin haya da zasu rika aiki a Kaduna dole su yi fentin ruwan kwai da baki, haka kuma waɗanda ke aikin tasi-tasi.
– Babu siyar da mai a jarkoki a kananan hukumomin Birnin Gwari, Kauru, Kachia, Kajuru, Chikun Giwa, Igabi, Kagarko.
– An hana safarar itace da gawayin girki a motoci, shiga ce ko fita.
– An dakatar da cin kasuwannin mako-mako a kananan hukumomin Igabi, Birnin Gwari, Giwa, Kajuru da babbar kasuwar mako-mako da ake ci duk Talata ta Kawo.
Gwamnati ta ce an ɗauki wannan makati ne domin a jama’a ba don son rai ba.
” Wasu mutane ƙalilan sun jefa mutane da yawa cikin halin ƙaƙanikayi babu gaira babu dalili. Ba za a bari hakan ya ci gaba ba, dole a bi duk hanyar da za abi a kawo harshen wannan masifa a ƙasar nan.
Discussion about this post