WATA SABUWA: Hukumar tara haraji za ta fito da ƙudirin karɓar haraji daga manyan motocin dakon kaya

0

Shugaban Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa (FIRS), ya bayyana wa Majalisar Tarayya cewa kuɗin da hukumar ke son tarawa daga haraji a cikin 2022, har naira tiriliyan 10.1, ba za su ko isa a gyara titinan Najeriya da su ba.

A kan haka ne Mohammed Nami ya shaida wa Kwamitin Harkokin Kuɗaɗe a Majalisar Tarayya cewa Hukumar FIRS za ta bijiro da wani ƙudiri ga majalisa, wanda za ta yi roƙon ya zama doka.

Ƙudirin a cewar sa, zai nemi a kafa wata doka da za ta fito da karɓar kuɗaɗen haraji ga manyan motocin ɗaukar kaya, waɗanda Nami ya kira “trucks”, domin a ƙara tara kuɗaɗen da za a riƙa yin aikin gyaran titina da su a ƙasar nan.

Ya shaida wa kwamitin cewa, “idan aka kafa dokar, za a iya riƙa tare manyan motocin a kan hanya, ba ma sai lallai a bakin shingen ‘tollgate’ ba, ana karɓar kuɗaɗe a hannun su.”

Ya ce ya tabbatar akasarin waɗannan motoci ba su biyan haraji duk kuwa da su na amfana da titinan gwamnati, waɗanda aka gyara da kuɗaɗen al’umma.”

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda za a dawo da harajin karɓar kuɗaɗe a shingayen kan titi, wanda Ministan Ayyuka Raji Fashola ya ce za a dawo da karɓar kuɗaɗen a kan titinan Gwamnantin Tarayya na faɗin ƙasar nan, masu tsawon kilomita 35,000.

Fashola ya ce kwanan nan Gwamnatin Buhari za ta gina shingayen karɓar haraji daga direbobi a manyan titinan Najeriya.

Gwamnatin Tarayya ta amince a fara gina shingayen karɓar haraji daga motocin haya da waɗanda ba na haya ba a kan manyan titinan Najeriya.

Ministan Ayyuka Raji Fashola ne ya shaida wa manema labarai haka, a Fadar Shugaban Ƙasa, jim kaɗan bayan kammala taron mako-mako na Majalisar Zartaswa (FEC), ranar Laraba, a Abuja.

Fashola ya ce an zartas da sake dawo da karɓar haraji daga masu motocin ne bayan an yi shawarwari da tuntuɓar masu ruwa da tsaki na ciki da wajen gwamnati.

Cikin 2019 ne dai Gwamnatin Buhari ta bayyana aniyar dawo da karɓar kuɗaɗen. Sai dai kuma bisa dukkan alamu ɓarkewar cutar korona a farkon 2020 ya haifar da cikas wajen aiwatarwa a baya.

Fashola ya ce duk da a baya gwamnati ta rushe shingayen karɓar haraji a kan titina, amma dai babu wata doka da ta haramta sake dawo da su.

Ministan ya ce tuni an yi bincike domin yanka farashin kuɗaɗen da ko waɗanne nau’in motoci za su riƙa biya.

Ya ce kuma an tantance wuraren da za a gig-gina shingayen.

“Ba wai daga gobe za a fara karɓa ba, amma dai an cimma babbar matsaya a taron yau Laraba.”

Ya ce za a fara da zaran an kammala gyaran manyan titinan Gwamnantin Tarayya. Kuma a kan manyan titinan ‘Express Way’ kaɗai za a yi.

Fashola ya ce manyan titinan da ke ‘dual carriage’, irin na Kano zuwa Abuja, yawan su ya kai tsawon kilomita 35,000 a faɗin ƙasar nan.

Share.

game da Author