Hukumar Daƙile Cututtuka ta Ƙasa (NCDC), ta bayyana cewa korona samfurin ‘Delta Varient’ mai saurin kisa, ta kashe mutum bakwai kuma ta kama mutum 1,149 a ranar Labara a faɗin ƙasar nan.
NCDC ta bayyana haka da safiyar Alhamis a shafin ta na yanar gizo.
Sai dai kuma alƙaluman sun nuna cewa an haɗa da adadin mutum 393 da su ka kamu da cutar a ranar Talata, a Jihar Legas.
Wannan adadin mutum 1,149 da su ka kamu, ya nuna cewa cutar korona samfurin ‘Delta’ na fantsama sosai.
A ranar Talata dai an samu ƙididdigar mutum 357 banda alƙaluman Jihar Legas.
NCDC ta danganta yawaitar fantsamar cutar da rashin yi wa jama’a masu yawa allurar rigakafin korona.
Haka kuma NCDC ta ce a yanzu akwai mutum 14,619 waɗanda hukuma ke sane da cewa su na ɗauke da korona yanzu haka a ƙasar nan.
Hakan na nufin ba a san yawan sauran kamammun da ba a auna ba, ballantana a ƙididdiga su cikin yawan waɗanda su ka kamu.
Kisan mutum bakwai da korona ta yi a ranar Laraba, ya kawo yawan waɗanda ta kashe a ƙasar nan zuwa mutum 2,236.
Rabon da a samu adadin da korona ta kama masu yawa kamar na ranar Laraba, tun cikin watan Fabrairu.