LEMAR PDP TA KAMA WUTA: Jiga-jigan jam’iyya takwas sun yi murabus, sun bar gwamnonin su da kururuwar neman gudummawa

0

Kwana ɗaya bayan jiga-jigan jam’iyyar PDP su bakwai sun ajiye ayyukan su na shugabancin jam’iyya a matakai daban-daban na ƙasa, an samu tsohuwar Sanata Joy Emordi, ɗaya daga cikin Shugabannin Kwamitin Amintattun PDP ta koma jam’iyyar APC.

Sai dai kuma duk da wannan koma baya da PDP ta samu,gwamnonin jam’iyyar sun roƙi a kwantar da hankali kuma a kai zuciya nesa, za su kyara wa gobarar ruwa su kashe wutar.

Gwamnan Sokoto kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP, Aminu Tambuwal ne ya yi kiran a Abuja.

Yayin da ya ke jaddada cewa za su shawo kan lamarin, Tambuwal ya ce PDP ce jam’iyyar da ƙasar nan ta zura wa ido tare da fatan za ta saisaita damalmalawar da mulkin APC ya yi wa Najeriya.

Waɗanda Su Ka Ajiye Muƙaman Su:

Masu riƙe da muƙamin mataimaka a muƙamai bakwai ne su ka ajiye aikin su a ranar Talata, daga Babban Kwamitin Zartaswar PDP.

Akwai Mataimakin Sakataren Yaɗa Labaran PDP na Ƙasa, Diran Odeyemi; Mataimakin Mashawarci a Fannin Shari’a, Ahmed Bello; Mataimakiyar Shugabar Mata, Hadizat Umoru da kuma Mataimakiyar Mai Binciken Kuɗi, Divine Amina Arong.

Sai kuma Mataimakin Sakataren Tsare-tsare, Hassan Yakubu; Mataimakin Sakataren Kuɗi, Irona Alphonsus.

Dukkan su sun ce sun sauka ne saboda zargin su cewa Shugaban Jam’iyya Uche Secondus bai iya tafiyar da shugabancin jam’iyyar bisa yadda ya dace ba.
[21:04, 8/4/2021] Ashafa Daughter Numbers: Yayin da Joy Emordi, tsohuwar Sanata wadda ke cikin waɗanda su ka ajiye muƙamin su ta koma APC, ita ta bayyana cewa ta fice daga PDP ne saboda rashin cancanta da rashin iya tafiyar da jam’iyya a hannun Uche Secondus.

Sanata Emordi dai ‘yar Jihar Anambra ce. Ta shiga APC watanni kaɗan bayan wasu gwamnoni biyu sun koma APC.

Share.

game da Author