Iyaye na ba su taya ni harkar noma, gani su ke yi aikin wahala na ke kawai -Inji mai digirin da ta rungumi noma

0

Bayan Rose Suberu ta kammala digiri na farko a Jami’ar Legas, sai ta kama noman masara gadan-gadan a cikin 2016. Daga nan kuma sai na ƙara himma ta riƙa noman kayan miya a Jihar Ogun.

“Bayan na gama digiri na farko, sai na kama aikin sakatariya a wani kamfani. Da na ga aikin dai ba wani daɗin sa na ke ji ba, sai na yi tunanin gara kawai na kama harkokin noma.

“Da farko sai na fara neman gona. Da na samu, sai na fara noman masara da kuma rogo. Da farko abin bai yi tasiri sosai ba. Amma saboda na ƙudurta a rai na cewa ba zan yi aiki a ƙarƙashin kowa ba. Sai na jajirce kawai.

Sai na fara binciken yadda zan bunƙasa harkokin noma na. Ina cikin bincike, sai na samu inda ake bayar da horon koya dabarun noma. Nan da nan na yi rajista. Bayan na gama samun horo, sai na kama noma kayan miya, irin su alayyahu da sauran su.

“A yanzu haka ina noma gonakin da faɗin su zai kai kadada 16, kuma duk na aro ne. Kuɗi na ke biya duk shekara ina nomawa.

“To ni dai a yanzu ba ni fuskantar matsalar tsaro. Amma dai ina taka-tsantsan sosai. Duk da haka ɗin ni dai makiyaya ba su taɓa kai min hari a gona su ka lalata min amfanin gona ba.

“Ina noma barkono, gurji da su tumatir da sauran su. Ina da masu saye tun a gona. Amma dai mafi yawa ina kaiwa kasuwar Mile 12 da ke Legas ina ba kwastomomi na a can. Amma yanzu na gane gara kawai na riƙa sayarwa a kasuwannin kusa da gona ta. Shi ya sa na ke kaiwa ina sayarwa a kasuwannin Ibadan.”

An tambayi Suberu yadda ta ke gaganiyar harkar noma, a matsayin ta na mace. Sai ta ce, “ai ni tinƙaho ma na ke yi da harkar noma, a matsayi na na mace. Ni ba wata ‘yar ƙwalisa ba ce, ballantana a ce min ina jin kunyar a ce ina noma.”

Suberu ta ce ta ɗauki ma’aikata shida masu yi mata aiki a gona. Kuma duk mutane ne da su ka san mutuncin kan su da mutuncin jama’a. Da sun gan ni, sun san aiko ya zo kawai.

“Babban ƙalubalen da na ke fuskanta shi ne rashin babban jari. Da kuma masu yi min aiki da yawa.

“Sannan kuma a gida ba a taimaka min, saboda gani kowa ke yi babu wata riba a harkar noma. Ni da ke yi, gani su ke yi wahala kawai na ke ci.”

Suberu ta ce ita mamba ce ta Adeniyi Cooperative Society. Ƙungiya ce ta manoma, wadda har yanzu ban fara cin moriyar ta ba. Saboda ban daɗe da shiga ba. Amma waɗanda su ka daɗe a ciki, a baya sun ci moriyar ta.”

Suberu ta ce a yanzu kayan noma na zamani ta fi buƙata, ba kuɗi ba.

Share.

game da Author