Gwamnati ta fara binciken yadda fuskokin fatara su ke a Najeriya – Minista Sadiya

0

Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta bayyana wani safiyo da ta ke yi kan yadda fatara ta ke ta fuskoki daban-daban a ƙasar nan (Multidimensional Poverty Index (MPI) Survey).

Minista Sadiya Farouq ce ta ƙaddamar da safiyon na MPI ta hanyar yanar gizo a ranar Talata.

A lokacin ƙaddamarwar, ministar ta ce Nijeriya ta bi sahun ƙasashe da su ka fara inganta hanyoyin su na yanke shawarar gudanar da shirye-shirye ta hanyar amfani da bayanan da aka samu daga binciken na MPI.

Ta ce, “Kowa ya amince a yi aiki da tsarin MPI ne saboda hanyoyi daban-daban da kuma yarjejeniyoyin ƙasashen duniya da aka yi, ciki har da Muradan Cigaban Ƙarni na Duniya, wato ‘Millennium Development Goals’ (MDGs), waɗanda an maye gurbin su da Muradan Cigaba Masu Ɗorewa, wato ‘Sustainable Development Goals’ (SDGs) domin su shafo sassa daban-daban na rashi wanda shi ne ruhin fatara da abubuwa masu alaƙa da ita.

“Saboda haka abin farin ciki ne mu tafi tare da sauran muryoyi masu ƙarfi wajen hasko muhimmancin aiki da masu ruwa da tsaki daban-daban a kan yaƙi da fatara, kawar da yunwa, bada nagartaccen ilimi, matakan yanayin ƙasa da kuma rungumar kowa, waɗanda dukkan su muhimman abubuwa ne wajen shaidar da MPI ke samarwa.”

Sadiya Umar Farouq ta lura da cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu nasarar inganta rayuwar sama da mutum miliyan 10 ta hanyar fidda su daga matsananciyar fatara ta hanyar ɗimbin shirye-shiryen gwamnatin, waɗanda su ka haɗa da shirin inganta rayuwa na ƙasa, wato ‘National Social Investment Programme’ (NSIP), da GEEP, Npower, NHGSFP da wasu da dama.

Ta ce, “Wannan muradin ya na yin la’akari da yawan jama’ar da ƙasar nan ta ke da shi yanzu wanda ya kai kimanin mutum miliyan 200, da kuma buƙatar samar da ingantacciyar shaida don tsara shiri.

“Don haka Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta tsaya tsayin daka wajen yin haɗin gwiwa da hukumomin gwamnati daban-daban, da ƙungiyoyin bada agaji da kuma masu zuba jari masu zaman kan su domin sa hannu a shirye-shirye tare da tabbatar da tasiri ga aiki ta hanyar bayanan da aka tattaro daga MPI don tabbatar da gaskiyar gwamnati ga al’ummar ƙasa ta hanyar ingantaccen sa-hannu ga shirye-shiryen gwamnati ta fuskoki da dama waɗanda za su tumɓuko tushen fatara.

“Bugu da ƙari, ma’aikatar za ta haɗa gwiwa sosai da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, wato ‘National Bureau of Statistics’ (NBS), domin gudanar da bincike a kai a kai a kan fatara ta hanyoyi daban-daban tare da yadda ake kashe kuɗi a matakan ƙasa baki ɗaya da na jihohi don tabbatar da matsayin da fatara ta ke a Nijeriya kuma a yi amfani da abin da aka binciko wajen gudanar da wani shiri ko tsari na gwambati.”

Ma’aikatar za ta haɗa gwiwa da mutane ‘yan kasuwa ko kamfanoni ta hanyar yin amfani da hanyar musamman ta shirye-shiryen haɓaka rayuwa don a ƙirƙiro wata taswira ko na’urar bin diddigi ta fatara a matakin ƙasa da na jiha wanda hakan zai taimaka wajen samar da cigaba a ƙudirorin rage fatara.

Haka kuma za ta haɗa gwiwa da Ma’aikatar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare na Ƙasa ta hanyar amfani da bayanan MPI don inganta rarraba kasafi ga sashe da jiha don kai wa ga mutane da ƙauyuka da gundumomi masu tsananin buƙatar kulawa.

Ministar ta gode wa Bankin Duniya, UNDP, OPHI, UNICEF, Ofishin Jakadancin Kanada, da sauran hukumomin ƙasa da ƙasa saboda tallafin da su ke bayarwa wajen kawar da matsananciyar fatara ya zuwa shekarar 2030.

Manyan baƙi da su ka bada saƙwannin goyon baya a taron sun haɗa da Kakakin Majalisar Wakilai, Rt Hon. Femi Gbajabiamila, wanda Hon. Sanusi Garba Rikiji ya wakilta, da kuma Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed, da Ƙaramin Ministan Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa, Prince Clem Agba, da Babban Jakaden Kanada a Nijeriya, da Wakilin Ƙasa na UNDP, Mista Mohammed Yahaya, UNICEF,
da Daraktan OPHI, Shugaban Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), Dakta Yemi Kale, da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Al’amuran Tattalin Arziki, Ambasada Yemi Dipeolu, da Sabine Alkire daga Jami’ar Oxford, da Kodineta na Ƙasa na ofishin tallafa wa al’ummar ƙasa, wato ‘National Social Safety Nets Coordinating Office’ (NASSCO), Mista Iorwa Apera.

Share.

game da Author